1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samun dorewar zaman lafiya a Gaza

August 28, 2014

Nahiyar Turai za ta taka muhimmiyar rawa domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/1D3Eq
Hoto: DW/K. Shuttleworth

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce dolene kasashen nahiyar Turai su taka rawar da ta dace domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Zirin Gaza ta hanyar sasanta rikicin da ke takanin Isra'ila da Palasdinawa. Hollande ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, inda ya ce kasashen na Turai ba za su iya ci gaba da kasancewa bankin da za a dogara da shi wajen sake gina inda aka ruguza sakamakon yaki ba. An dai cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ba a bayyana wa'adin karewarta ba tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas bayan da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fuskanci gagarumar suka da kuma matsin Lamba a cikin gida sakamakon yakin da ya kwashe kwanaki 50 yana yi da Palasdinawan, wanda kuma har kawo ga tsagaita wutar babu bangaren da ya yi galaba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu