1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari a jihar Kano da ke Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 17, 2014

Mutane da dama sun hallaka yayin da wasu kuma suka jikkata, sakamakon wani mummunan hari da aka kai kwalejin ilimi ta Tarayya da ke jihar Kano a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1DES5
Hoto: Reuters

Rahotanni daga jihar ta Kano da ke yankin arewa maso yammacin Tarayyar Najeriya na nuni da cewa akalla mutane15 ne kawo yanzu aka tabbatar da cewa sun hallaka, sakamakon wani hari da aka kai kwalejin ilimi ta gwamnatin Tarayya da ke jihar wato FCE Kano. Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe biyu na Laraban nan bayan da wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a kwalejin yayin da dalibai ke tsaka da daukar darasi. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wasu mutanen 34 kuma sun samu raunuka. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai jami'an tsaro a jihar na zargin 'yan kungiyar Boko Haram da aikata wannan aika-aika.