1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin hare-hare a Wukari-Taraba

April 16, 2014

Rayuka masu yawa sun salwanta, a yayin da aka kafa dokar hana fita, sakamakon harin 'yan bindiga da ya auku a daren ranar Talata a garin na Wukari.

https://p.dw.com/p/1BjKp
Nigeria Soldaten
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Rahotanni daga jihar Taraba da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewar, rayuka da dama aka rasa cikin daren Talata, a garin Wukari sakamakon hare haren da wasu 'yan bindiga suka kai a kauyen Nwunkyo-Kura cikin daren jiya Talata.

Tuni dai gwamnatin jihar ta kafa dokar hana yawo ba dare ba rana a garin na Wukari, sakamakon dauke daren jiyan da aka yi ana kashe-kashen da har kawo yanzu ba a kai ga tantance yawan wadanda suka mutu ba.

Wani mazaunin yakin ya shidar dacewar mutane da dama sun mutu, sai dai babban abinda ya fi zama tashin hankali shi ne, yadda sojoji suka kauracewa yankin gabanin faruwar harin.

Tuni dai kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Taraba DSP Joseph Kwaji ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin na garin Wukari.

Mawallafi : Muntaqa Ahiwa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar