1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabanin bayanai a kan 'yan matan da aka sace

April 17, 2014

Rundunar tsaron Najeriya ta ce ta kubutar da yawancin dalibai mata da aka sace a makarantar Chibok ta jihar Borno. Amma iyaye da ‘yan uwa suka ce har yanzu ba su ga ‘ya‘yan nasu ba.

https://p.dw.com/p/1BkTD
Hoto: AFP/Getty Images

Sojojin sun yi ikirarin karbo 'yan mata 121 da a ka sace, in ban da takwas da ke hannun ‘yan bindiga. Sai dai a yanzu iyaye na nuna shakku saboda har yanzu ba su ga 'ya'yan nasu ba. Hasali ma dai iyaye na ci gaba da neman inda ‘ya'yansu suke ban da guda goma sha hudu da gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ba da tabbacin cewa an samesu. Gwamman ya kuma yi shailar bayar da tukuycin kudi Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanai da suka kai ga gano ‘yan matan.

Tuni mutane sama da hamsin suka yi rejistar rashin ganin ‘ya‘yansu. Ana zaton cewar wasu karin iyaye ma zasu yi rajistar. Wannan yanayi ya haifar da rudani da damuwa tsakanin iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki, abinda ya hana da damansu cin abinci ko ma samun isasshen barci saboda ba su san halin da ‘ya‘yansu ke ciki ba.

Gazawar jami'an tsaro na kare rayuka

Wannan yanayi da aka shiga na rashin sanin gaskiyar inda wadannan ‘yan mata suke na kara nuna gazawar jami'an tsaro da gwamnatin Najeriya na neman murkushe kungiyar Boko Haram wacce aka kwashe shekara biyar anan fafatawa da ita. Akwai masu ganin cewa kame wadannan ‘yan mata ma wata makarkashiya ce na neman jaddada dokar ta baci da hukumomin Najeriya suka yi.

Afrika Kinder lachen
Mata 'yan makaranta na shiga tarkon 'yan bindiga a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Yanzu haka dai iyaae sun bazama dazuka domin nemo ‘ya‘yansu a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen kasar na gano wadannan dalibai mata.

Mawalafi: Al-Amin Muhammad daga Gombe
Edita: Mouhaadou Awal Balarabe