1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a Majalisar dokokin Afirka ta Kudu

August 22, 2014

Majalisar dokokin Afrika ta Kudu ta ce za ta binciki musabbabin rudanin da mambobin jam'iyyar da ke da manufofin kare tattalin arziki ta EFF suka haifar a kann gidan Zuma ba.

https://p.dw.com/p/1CzVO
Jacob Zuma wiedergewählt
Hoto: Rodger Bosch/AFP/Getty Images

Majalisar dai ta dau matakin bincikar wannan rudanin ne bayan da jagoran jam'iyyar ta EFF Julius Malema da magoya bayansa suka yi ta kururuwa a zaman majalisar na Alhamis din da ta gabata, inda suka yi ta kira ga shugaba Jacob Zuma da ya dawo da wasu makudan kudade da aka kashe wajen kwaskwarima ga wani gidansa a garin Nkandla.

Südafrika Economic Freedom Fighters 21.08.2014
Rudanin da 'yan jam'iyyar EFF suka yi a majalisa ya sa su artabu da 'yan sanda.Hoto: Reuters

Da fari dai mataimakiyar kakakin majalisar ta bukaci masu ihun yayin zaman majalisar da su fice, ko da suka ki sai aka nemi 'yansanda su shigo dan fitar da su. Tuni dai al'ummar kasar suka nuna rashin amincewarsu da wannan mataki da shugabancin majalisar ya dauka kan 'yan majalisar na jam'iyyar EFF.

Ita ma dai jam'iyyar DA wadda ita ce babbar jam'iyyar adawa a kasar irin mataki daya ta ke kai da jam'iyyar ta EFF inda ta ke cewar kyautuwa ya yi a ce Shugaban Zuma ya dauki nauyin wannan kwaskwarima ta gidansa da kashin kansa saboda gudun abin da zai je ya dawo.

Jam'iyyar ANC ta Shugaba Zuma a nata bangaren kuwa cewa ta yi wannan rudani da 'yan jam'iyyar EFF din suka haifar yunkuri ne na zubar da kima ga dimokradiyar wannan kasa ta Afrika ta kudu wacce ANC ta dauki lokaci mai tsawo ta na ginawa yayin da a hannu guda masharhanta da sauran al'ummar kasar ke ganin ANC din ce da kanta ke yunkuri na rushe kimar dimokradiyar kasar da kanta.

Mandela Trauerfeier Johannesburg 10.12.2013
Shugaba Zuma na fuskantar matsin lamba tu bayan da aka yi amfani da kudin gwamnati wajen kwaskwarimar gidansaHoto: Reuters

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Ahmed Salisu