1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Boko Haram da zabe a Najeriya

Mohammad Nasiru AwalFebruary 6, 2015

Rikicin Boko Haram da babban zabe a Najeriya da kuma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1EXK1
Anschlag in Gombe, NIgeria 02.02.2015
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

A labarinta mai taken sojojin Chadi na yaki a Najeriya jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun yi asarar wani gari mai muhimmanci sakamakon gumurzu na tsallaken iyaka, sannan sai ta ci gaba da cewa.

A karon farko sojojin Chadi sun fatattaki kungiyar Bokom Haram daga garin Gamboru mai yawan mutane kimanin dubu 85 wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru bayan wani mummunan fada. Jaridar ta ce masu kaifin kishin Islama da sauran fararen hula sun tsere daga garin na Gamboru wanda wata gada mai tsawon mita 500 da ta ratsa kan wani kogi, ta raba da garin Fotokol na arewacin Kamaru. Bayan an fatattakesu daga Gamboru mayakan Boko Haram sun shiga garin Fotokol inda a can din ma suka kwashi kashinsu a hannu. Kutsen da sojojin na Chadi su kimanin 2000 suka yi a Gamboru shi ne matakin farko na yakin da sojojin Chadi ke yi a yankin Najeriya.

Tarzoma a yakin neman zabe

Wahlkampf in Nigeria 2015
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Zaman dar-dar a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir har wayau inji jaridar ta Die Tageszeitung tana tsokaci a kan tashe-tashen hankula masu nasaba da zaben da ke tafe a Najeriya.

Ta ce kawo yanzu yankin na Niger Delta ya kasance hannun jam'iyyar PDP ta shugaban kasar Goodluck Jonathan wanda dan yankin ne. Amma an fara ganin alamun sauyin abubuwa, abin da ya haddasa tsoro a zukatan shugannin jam'iyyar. Jaridar ta ce yankin da ma wasu yankuna a tarayyar ta Najeriya sun zama dandalin tashe-tashen hankula a yakin neman zaben na ranar 14 ga watan Fabrairu. Jaridar ta rawaito fashewar bama-bamai a gine-ginen wasu kotuna da ke jihar Rivers a wannan mako da kuma wanda aka samu musamman a garin Gombe. Wannan dai lamari ne mai tayar da hankali da sanya fargaba a zukatan dukkan 'yan Najeriya masu kaunar ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Koma bayan tattalin arziki sakamakon Ebola

Ita kuwa mujallar Handelsblatt ta mayar hankali ne a kan cutar Ebola da asarar kudade masu yawa da ta janyo wa kasashen Afirka musamman a harkar yawon bude ido.

Sierra Leone Ebola
Hoto: REUTERS/Baz Ratner

Ta ce cutar Ebola mai saurin kisa na ci gaba da sanya tsoro ga masu sha'awar zuwa yawon bude ido a Afirka, duk da cewa mafi yawan kasashen da ke tafiyar da harkar yawon bude idon suna nesa da yankuna masu fama da cutar. Jaridar ta rawaito kamfanonin shirya tafiye-tafiye na korafi game da koma bayan ciniki musamman wanda ya danganci masu na 'yan yawon shakatawa a Afirka.

Shakku game da zaman lafiyar Sudan ta Kudu

Rattaba hannu maras daraja inji jaridar Der Tagesspiegel sannan sai ta ce kwana guda bayan shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da abokin gabarsa Riek Machar sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, fada ya sake barkewa a kasar. A ranar daya ga watan nan na Fabrairu mutanen biyu suka amince da shirin tsagaita wuta karo na hudu a gaban kungiyar IGAD a kan kafa gwamnatin raba madafun iko kafin watan Yuli. Amma kasancewa a baya ma an yi wannan yunkurin ba tare da samun biyan bukata ba, a wannan karon ma ba mai sa ran ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu.