1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici Iraki na ci gaba janyo mutuwa

October 1, 2014

MDD ta bayyana adadin wadanda suka hallaka a Iraki cikin watan jiya

https://p.dw.com/p/1DOIk
Syrien - Kurden in Kobane
Hoto: Getty Images/B. Kilic

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 1,200 suka hallaka sakamakon rikicin Iraki a watan jiya na Satumba. Rahoton majalisar na wannan Laraba bai kunshi adadin mutanen da suka rasa rayukansu a yankunan da ke karkashin kungiyar mai neman kafa tsarin Islama ta IS ba.

Masu kaishin addinin Islama sun hallaka 'yan kasar masu yawa. Kasar tana fuskantar rikici mafi muni tun bayan janyewar dakarun Amirka a karshen shekara ta 2011. Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bayyana cewa kusan 'yan kasar ta Iraki 2000 suka samu raunika.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane