1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tsaro na jawowa Najeriya asara mai yawa

April 23, 2014

A Najeriya koma bayan da kasuwar hada-hadar hannayen jarri ke fuskanta daya sanyata asarar Naira bilyan 392 saboda matsalolin da suka hada da na rashin tsaro ya na kawo damuwa.

https://p.dw.com/p/1BnYW
Abuja Bombenanschlag 14.4.2014
Hoto: imago/Xinhua

Wannan mumunan koma bayan da kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ke ci gaba da fuskanta da ya faro tun a 2008 lokacin da tattalin arzikin duniya ya shiga mummunar matsala, abinda ya sanya sanya farashin mafi yawan hannayen jarin ci gaba da tuntsuarawa a cikin kasar daga watan Janairun wannan shekara ta 2014 zuwa yanzu, na zama abinda masana tattalin arziki da zuba jari ke bayyana cewa ma'uni ne da ke nuna halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Ko da yake ana dangata wannan matsala da dalilai na rashin tsaro da kasar ke fuskanta wanda ya sanya kai hare-hare na bama-bamai abinda ya sanya masu zuba hannun jari da dama ja baya daga harkokinsu yayinda a shekarun baya wasu kamfanonin suka tattara nasu ya nasu suka fice daga kasar saboda matsaloli mabanbanta, amma ga Malam Ahmed Manu dake hada-hadar hanayyen jari a kasuwar da ke Abuja ya bayyana yadda suke kallon lamarin.

‘'Kasan zancen kasuwa a ko da yaushe abinda ke janyo ta yi kasa ko sama shine batun kudi, da ake amfani dasu wajen hada-hadar hannayen jari, sannan kuma akwai matsalar rashin tsaro shima yana sa tayi kasa, sannan akwai batun manufar gwamnat,i domin idan yan kasuwa basu san inda gwamnati ta dosa ba wannashima yana shafa, koda a manyan kasashe. Domin ita kasuwar hannayen jari ma'auni ne ko mizani na yanayin da tattalin arzikin kasa yake don haka koma bayansa na da illa sosai''.

A shekarun baya dai kasuwar hannayen jarrin Najeriyar ta kasance tamkar wata zarkadadiyar budurwar da ake ta zarya domin zuba jari a cikinta, saboda kasancewarta wacce ake samun riba ninki ba ninki idan aka kwatanta da na wasu kasashen ketare. To sai dai koma bayan da take ta fuskanta ya sanya jefa shakku ga masu wannan sana'a da ta zama hanya mai sauki ga yan boko da ma masu karamin karfi na samun kudi musamman a shekarun baya-baya a cikin kasar.

Symbolbild Gewalt in Nigeria
Rashin tsaro a NajeriyaHoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

Sanin muhimmancin kasuwar hannayen jarii da ke nuna lafiya ko karfin masana'antu a kasar ya sanya tambayar illar da hakan ka iya yi ga tattalin arzikin Najeriyar da amakwanin baya ne aka bayyana shi a matsayin wanda yafi kowane karfi a nahiyar Afrika, amma ga Malam Abubakar Ali na cewa akwai fa abin dubawa a kan wannan.

Amma ga Malam Amadu Manu kwararre a harkar hada-hadar hanayyen jari yace abinda yafi tada hankalinsu shine yadda har yanzu ba'a sanya kamfanonin sadarwa a cikin wadanda ake hada-hada a kasuwannin hannayen jarin kasar.

‘'Abinda yasa ta bunkasa rashin kyakkyawar tsarin tattalin arziki da kuma rashin ilimin hannun jarri ga al'umma ‘'

Koma da tuntsurawar da harakar kasuwar hannayen jarin Najeriyar ke fuskanta dai na zama wanda ke shafar sashin tattalin arzikin Najeriya, sai dai wkarrau na bayyana cewa akwai kyakyawar fatan ta samun bunkasar lamarin bisa ga maiznin tattalin arzikin Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu