1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashawa na jimamin kisan Nemtsov

Usman Shehu UsmanMarch 1, 2015

Dubban 'yan kasar Rasha na yin maci don jimamin mutuwar Boris Nemtsov wani sananne a sukar gwamnatin shugaba Vladimir Putin

https://p.dw.com/p/1E0uw
Russland Oppositioneller Boris Nemzow erschossen
Hoto: Kirill Kudryavtsev/AFP/Getty Images

Kisan gilla da aka yiwa fitaccen dan adawan kasar ta Rasha Boris Nemtsov, ya kada zukatan al'ummar kasar da jawo martani daga shugabannin duniya.

Fitacccen mai sukar gwamnatin kasar ta Rasha Boris Nemtsov, ya gamu da ajalinsa ne, bayan da ya ci abinci ya kama hanyarsa a kusa da fadar shugaban kasar ta Kremlin, inda wani da ba a kai ga tantancewa ba, ya bude masa wuta har sau hudu. Don haka koda shi kansa shugaba Vladimir Putin, ya ce wanda ya aikata kisan kwararre ne, wanda aka yi hayarsa, kuma duk inda ya shiga gwamnati za ta zakuloshi. Sai dai kisan gillan ya zo 'yan sa'o'i bayan da mutumin ya yi kira ga Rashawa su fito a gangamin da aka shirya ranar Lahadi, don adawa da manufar gwamnatin Putin a kasar Ukraine. Don haka lamarin ke kawo ayoyin tambaya da yawa, kamar yadda wannan matar ke cewa a lokacin da ta je ajiye fure a wurinda aka yi kisan.

"Ni lamarin ya kasance mini tamkar ni ya samu, tamkar wani dan una ne aka hallaka. Daga jin mutuwar sai na fara kuka. Mutumin kirki ne, dan siyasa ne na kwarai, amma ga mutuwarsa ta zo da mummunan yanayi"

A yanzu dai shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da bincike kan mutuwar, inda kuma ya ce shi kansa ne zai jagorancin binciken, domin an yi hayar wasu ne bisa kawo rudanin siyasar kasar, kamar yadda kakakin shugaban ya sanar.

"Na farko dai muna ganin an yi kisan ne, don tada hankalin, a kawo rudani a kasar. Wani shiri ne da ke da alaka da rikicin kasar Ukraine. Ba abun boye ba ne, akwai masu tsattsauran ra'ayi da babu wani mutum mai fada su saurare shi"

Wasu 'yan adawa a siyasar kasar dai, tuni suka dorawa shugaba Putin alhaki, suna masu cewa ya yi hakanne domin wata manufar siyasa. Haka shima masanin siyasan Nikolai Swanidse yake cewa.

"Daya daga cikin dalilan da za su a yi sa irin wannan kisan gikllar, shi ne tsauraren matakai da ake dauka, wadanda muke ganin ana dauka, bisa yancin fadin albarkacin baki da kafafen yada labarai"

Boris Nemtsov dai baya boye adawarsa ga shugaba Putin, musamman yanzu da ake zargin Rasha na da hannu a rikicin gabashin kasar Ukraine. Inda sa'o'i uku gabanin mutuwarsa, ya fada wa wani gidan radiyon Moskow cewa.

"Babbar matsalar da kasar mu ke fiskanta a yanzu, ita ce, mahaukatan manufofin Putin, da ya ke dauka a kasar. Inda aka dauki mummunar siyasa kan 'yan kasarmu, bisa yakin da ke faruwa a kasar kasar Ukraine"

Tuni dai shugabannin kasashen Yamma suka yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa Bors Nemtsov. Shugaban kasar Amirka Barack Obama, ya yi tir da kisan dan siyasa, kana ya bukaci da gwamnatin Rasha ta gudanar da bincike na hakika. Shi kuwa shugaban kasar Faransa François Hollande, yace wannan kisa ce ta kiyayya, wanda aka yi wa mai kare demokradiyya. Yayinda a nasa martanin Firaministan Birtaniya David Cameron, ya ce wannan kisan dabbanci ne, kuma dole a gaggauta gudanar da binciken da ba rufa-rufa.

Russland Tatort des Mordes von Boris Nemzow in Moskau (Bildergalerie)
Hoto: Oleg Matsnev
Russland Tatort des Mordes von Boris Nemzow in Moskau (Bildergalerie)
Hoto: Oleg Matsnev