1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta musanta kai sojinta Ukraine

Ahmed SalisuMarch 5, 2015

Rasha ta musanta ikirarin da ta ce Amirka ta yi na aikewa da dubban sojinta don agazawa dakarun 'yan aware da ke gabashin Ukraine wanda ke samun goyon bayan kasar ta Rasha.

https://p.dw.com/p/1Elda
Wladmir Putin Portrait Moskau Kreml
Hoto: Getty Images/AFP/A.Nikolsky

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan Rasha din Alexander Lukashevich ya ce wannan ikirarai da Amirka din ta yi abu da bai da tushe balle makama kuma ma abu ne da hankali ba zai dauke ba.

A jiya Laraba ce mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amirka din Victoria Nuland ta shaidawa wasu 'yan majalisar dokokin Amirkan cewar Rasha ta aike da dubban dakarunta Ukraine don yin yaki tare da 'yan aware ko da dai ba ta fadi hakikanin adadin da ta ce Moscow din ta aike ba.

Amirka da sauran kasahsen duniya dai sun sha zargin Rasha da hannu a rikicin na Ukraine wanda sanadinsa mutane dubu 6 suka hallaka, sai dai Rashan ta sha musanta wannan zargi.