1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotanni masu rikitarwa game da hatsarin Germanwings

Mohammad Nasiru AwalMarch 26, 2015

Binciken farko a kan hatsarin ya nuna cewa daya daga cikin matukan jirgin saman ya janyo faduwarsa.

https://p.dw.com/p/1Exwy
Flugzeug Airbus Cockpit
Hoto: Getty Images/A. Hassenstein

Yayin da ake ci gaba da binciken gano musabbabin faduwar jirgin saman kamfanin na Germanwings, jaridar New York Times ta rawaito cewa daya daga cikin matukan jirgin ba ya kan kujerarsa a dakin matukan wato Cockpit lokacin da jirgin ya fado. Jaridar ta rawaito wata kafar bincike a Faransa na cewa matukin ya bar dakin jin kadan da tashin jirgin kuma ya kasa komawa ciki, kuma duk da kwankwasawar da ya yi ta yi, abokin aikinsa bai bude masa kofar ba. Sai dai ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maizière da kamfanin Lufthansa da ma Germanwings ba su ce uffan ba game da wannan labari.

Sai dai wani labarin daga lauyoyin gwamnati a birnin Marseille da ke kudancin Faransa na cewa da gangan mataimakin matukin jirgin saman na Germanwings ya haddasa hatsarin. Brice Robin shi ne wakilin lauyoyin gwamnatin cewa yayi:

"Ina jin dai da gangan ya ki bude kofar ya kuma kunna na'urar da ta ka da jirgin."

A kuma halin da ake ciki majalisar dokokin Jamus a birnin Berlin ta tuna da wadanda hatsarin ya rutsa da su. Norbert Lammert shi ne kakakin majalisar.

"Muna mika ta'aziyarmu ga 'yan uwa da abokannen wadanda hatsarin ya rutsa da su. Tun bayan aukuwar wannan hatsarin, kasashen duniya sun yi ta yi wa Jamus jaje."