1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyi

Mohammed, ZainabJanuary 31, 2012

Muna farin ciki tare da marhabin da ra'ayoyin masu sauraro, dangane da shirinmu na Ji Ka Karu. Kuna iya aiko mana ta adireshinmu na E-mail ko kuma ta wasika.

https://p.dw.com/p/Enm1
Hoto: Das Fotoarchiv

Laminu Musa, Maraɗi, Jamhuriyar Nijer (mousslami@yahoo.com)

Na yi matuƙar farin ciki da shirinku na Ji ka Ƙaru akan mayar da duniya tsinsiya maɗaurinki ɗaya, musamman ma dai yadda kuka bayyana mana tsarin noman yarjejeniya, da kuma yadda ake ƙulla alaƙa tsakanin manoma da kuma manyan kamfanoni da suke cinikayyar amfanin gona da abinci.

Malam Ango Yawuri, Najeriya (mallanango@yahoo.com)

DW Allah ya saka muku da alheri, na yi farin ciki da shirin Ji Ka Ƙaru wanda akai batu game da tsarin mayar da duniya bai ɗaya. To amma tamabayata ita ce; Shin idan aka mayar da duniya bai ɗaya, kuɗi ɗaya duka ƙasashen duniya za su riƙa amfani da su ko kuwa yaya abin yake.

Kabir Sakaina layin ‘yan goro Malumfashi, Katsina Najeriya.

(kabeersakaina@gmail.com)

Shirinku na Ji Ka Ƙaru akan tsarin noma na adalci ba cuta ba cutarwa, shiri ne da yake da matuƙar ƙayatarwa da ilimanatarwa. Da fatan sashen Hausa na DW zai tsara dukkanin shirye-shiryenku na Ji Ka Ƙaru a faya-fayai da kaset-kaset ku aika ga gidajen rediyo da dama na jaridu da mujallu a nahiyar Afirka. Domin a gaskiya waɗannan shirye-shirye amfaninsu ba mai ƙarewa ba ne, don haka bai kamata a ce wadannan shirye-shirye masu ma'ana daga an watsa su sau ɗaya shi ke nan sun tafi ba.

Salamatu Yusuf Dodo Najeriya (salma12@yahooo.com)

DW Ina mai tabbatar muku da cewa, shirinku na Ji Ka Ƙaru ya sa kun zarce sa'a, mu dai a wajenmu ba ku da na biyu. Gaba dai gaba dai radiyo DW.