1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyi a kan garambawul gwamnatin Nijar

Abdoulaye Mamane Ahmadou daga YamaiFebruary 26, 2015

Bangarori daban daban na Jamhuriyar Nijar na bayyana matsayinsu kan nada mace Aishatou Boulama Kane da aka yi a matsayin sabuwar ministar harkokin wajen kasar.

https://p.dw.com/p/1EiDs
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

Ofishin ministan harkokin wajen Nijar ya tashi daga hannun Bazoum Mohamed tare da komawa hannun Aichatou Boulama Kane. Shi kuwa Bazoum an danka masa mukamin minista na musamman a fadar shugaban kasa.

Tuni dai kungiyoyin mata suka fara bayyana ra'ayinsu a kan nadin na sabuwar shugabar dioplomasiyar Nijar. Mme Aissata Bangna Fall shugabar kungiyar Transparency International ce a reshen Nijar kuma daya daga cikin abokan gwagwarmayar Aichatou kane Boulama a 1991. Ta ce sun " gode wa Allah da aka tuna da mace aka sakata a cikin wannan gurbi. Ya kamata mu yi murna."

Tarihin Aichatou Boulama kane
An haifi Mme Boulama a garin Keita na jihar Tahoua a shekarun 1955 inda ta fara karatunta a garuruwan Maine Soroa na jihar Diffa, tare da kammala wasu karance-karancenta na koli a kasar Faransa inda ta yi digirinta a fannin sufuri da tattalin arziki a birnin Paris a shekarun 1991.

Sitzung der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

Sabuwar ministar harkokin wajen Nijar ta wakilci mata a gagarumin taro na kasa "Conférence nationale" inda ta hanyar taimakon da ta bayar da karfin tuwo mata suka kwato ranar karrama mata ta kowace ranar 13 ga watan Mayu. Daga nan ne Mme Boulama ta fara shiga gwagwarmaya irin ta siyasa inda har ta rike mukamai da dama cikinsu har da babbar sakatariyar ofishin ministan fasali, da gwamnar birnin Niamey da kuma mukaminta na karshe na daraktar fadar firaministan Nijar.

Alhaji Moustapha kadi Oumani wani na kungiyoyin fararen hullar Nijar ya danganta Aichatou Boulama da "mace mai kamar maza da za ta iya fidda kitse daga wuta domin ta saba aiki a Jamhuriyar Nijar domin mace ce da aka yi tsamanin za ta kama ludayin firaminista."

Mohamed Bazoum ya samu sauyin matsayi
Mohamed Bazoum ya samu sauyin matsayiHoto: picture-alliance/dpa

Makomar Bazoum a fannin siyasa

Masu sharhi akan al'amurran yau da kullum na yi wa garanbawul din kallon tamkar wata dama ce ake son baiwa tsohon shugaban dipolomasiyar Nijar Bazoum Mohamed da ya dukufa domin inganta tafiyar da ayyukkan jam'iyyarsa ta PNDS-Tarayya mai mulki. Tun lokacin da aka zabeshi domin ya shugabanceta a watan Disamban bara bai taba zuwa ganawa da magoya bayan PNDS ba. Hasali ma wasu 'ya 'yan jam'iyyar suka ce basu taba ganinsa ba.