1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP ta amince da takarar Jonathan

Uwais Abubakar IdrisSeptember 19, 2014

Al'ummar Najeriya na tofa albarkacin bakinsu dangane da amincewa da jam'iyyar PDP mai mulki ta yi da Shugaba Jonathan a matsayin dan takara a zaben 2015.

https://p.dw.com/p/1DFnc
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan ne dai karon farko da jam'iyyar ta PDP da ta kwashe shekaru 15 tana mulki a Najeriyar ta amince wa mutum guda a matsayin dan takararta tun ma kafin a kai ga zaben fidda gwani. Amince wa Shugaba Goodluck Ebele Jonathan din a matsayin dan takara daya tilo a jam'iyyar ta PDP da ya faro tun daga yin hakan da gwamnonin kasar suka yi a cikin makon nan duk kuwa da nuna sha'awar takara da gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya yi wanda daga baya ya janye ba shiri babu zato ya sanya maida martani a kan wannan lamari.

Ba a bi tsarin dimokaradiyya ba

Wani dan siyasa Malam Imrana Wada na da ra'ayin cewa hakan ya saba wa tsari na dimokaradiyya ya kuma ce ba zai yi tasiri a wajen irinsu ba.

Porträt - Sule Lamido
Sule Lamido Gwamnan jihar Jigawa a NajeriyaHoto: Getty Images

Amma ga mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP Barrister Abdullahi Jallon cewa ya yi tsari na jam'iyyarsu fa yana cike da bin tafarkin dimokaradiyya, kuma fidda Shugaba Jonathan din a matsayin dan takara bai hana kowa ya fito ba.Tun kafin wannan lokaci dai magoya baya ke ta gangami na shugaban na Najeriya ya fito zabe a matakin da har yanzu bai ce uffan ba sai dai kawai ya ce ba zai kunyata masu bukatar ya yi hakan ba.

Ya cancanta ya tsaya ne

Malam Abdullahi Abubakar wani dan jam'iyyar PDP kuwa a nasa ra'ayin abin da ya faru siyasa ce kuma sun ga ya cancanta ne suka yi hakan ta hanyar tsayar da shi a matsayin dan takara. Abin jira a ganin shi ne inda guguwar siyasar Najeriyar da ke kadawa za ta dosa musamman ga zaben fidda gwani da jam'iyyar ta PDP ta sanya a gaba wato ranar shida ga watan Disamba mai zuwa da ma masu nuna dari-dari da yiwuwar gudanar da zabe a Najeriyar a 2015 duk kuwa da tabbacin hakan da hukumar zabe da ma gwamnatin ke bayarwa.

Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Jiga-jigan jam'iyyar PDP mai mulki a NajeriyaHoto: DW/U.Musa