1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na tunanin hadewa da wasu jam'iyyun adawa

Ubale Musa/PAWMay 18, 2015

Bacin wannan buri da ta sa a gaba, jam'iyyar da ta yi mulki na shekaru 16 a Najeriya ta ce ba za ta sauya sunanta, ko alamarta ba, duk da kaurin sunan da ta yi a baya

https://p.dw.com/p/1FRbn
Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Hoto: DW/U.Musa

Kasa da tsawon makonni biyu ga kaiwa ga adabo da mulkin tarrayar Najeriya na shekaru 16, tuni dai tasiri na asarar mulkin ya fara yin lahani a cikin jam'iyyar PDP da yanzu haka ke tunani na makoma.

Sannu a hankali dai zahiri na asarar mulki na dada tabbata cikin PDP mai mulki, sannu a hanakali kuma dafin yana dada tasiri a cikin jini dama tsokar jam'iyyar da ko bayan nasarar mulki ke fafutuka ta komarta cikin fagen siyasar kasar yanzu haka. Kama daga rikidewa da ma mantawa da alamar lemar ya zuwa ga kokari na rushewar kwamitin zartarwar, sannan da samar da sabbabi na shugabanni a gareta ya zuwa hadewarta da kananan jam'iyyu da nufin samar da adawar mai karfi dai lissafin yayi nisa cikin gidan na wadata da kai yake rabe a halin yanzu.

Yomi Osibanjo und Muhammadu Buhari (Nigeria APC)
Zababbun shugabanin APC da suka sanya PDP ta zama adawaHoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Yiwuwar hadewar PDP da kananan Jam'iyyu

Wata sanarwar jam'iyyar dai ta ce duk da PDP na nazarin yiwuwar hadewar ta da jam'iyyun da a baya suka taimaka wajen tabbatar da tasirinta irin nasu APGA da Labour Party, babu batun sauyin suna ko ta alama da nufin rikidewa a fadar kakakin na gidan na Wadata daya kuma a cikin masu fada ajin cikin jam'iyyar yanzu haka.

Oliseh Metuh dai ya ce PDP na iya hadiyar jam'iyyun da nufin kara mata karfi dama taka rawa da karsashi a adawar, amma babu tunanin rushe lema balle mantawa da sunan dake zaman mafi tasiri a zukata ta yan kasar kafin yanzu. Ra'ayin kuma da ya saba a tsakanin yayan jam'iyyun irinsu Bala bawa ka'oe dake zaman tsohon ma'ajin jam'iyyar na kasa da kuma ke kallon mafita na ga ajiye aikin su Oliseh tare da maye gurbi na shugabancin jam'iyyar domin farfado da suna da ma kimarta tsakanin yan zaben kasar ta Najeriya a nan gaba

Bukatar sauya "jini" a cikin jam'iyyar

Kokari na sauya jini cikin PDP ko kuma kokari na kara ta'azzara rikici ga masu gidan na wadata dai ana zargin shugabancin yanzu da karbar rashawar da ta kai daya a cikinsu har ga sayen jirgi sakamakon cuwa-cuwar da ta mamaye fidda gwanayen tsayawa jam'iyyar takara a zaben da ya shude. To sai dai kuma ko bayan hancin dai a tunanin Hamisu Mu'azu Shira da a baya ya yi nasarar taka rawa kafin daga baya ya sha gorar lemar dai na zaman rushe daukacin jam'iyyar da ma mantawa da duk wani abun da 'yan kasar ke iya ambata da kalmar lema kafin iya sake zubi dama kila samun nasara cikin gidan na wadata.

Nigeria Regierungspartei PDP
PDP ta ce ba za ta sauya wannan tambarin baHoto: DW/K. Gänsler

Alhaji Adamu Chiroma dai na zaman daya a cikin mutane uku na farkon fari da suka zauna suka yanke cibaya ga jam'iyyar can baya, kuma shi a ganinsa dogon jira dama karin hakuri na zaman karatun 'ya'yan PDP da suka share shekara da shekaru suna yin shagwaba, amma kuma suka samu kansu cikin tsakiyar kogi yanzu. Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba ga jam'iyyar, da ke shirin karbar ragamar ta adawa a cikin halin rikici da rabewar kai.