1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama na ta'aziyya a masarautar Sa'udiyya

Muntaqa AhiwaJanuary 27, 2015

Shugaban Amirka ya je taya sarki Salman na Sa'udiyya murna tare da jajenta wa masauratar kasar dangane da rasuwar marigayi sarki Abdullah bin Abdul'Aziz.

https://p.dw.com/p/1ERCB
Obama in Saudi Arabien 27.01.2015
Hoto: Reuters/J. Bourg

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya jagoranci manyan jami'an gwamnatin kasarsa da ma wasu 'yan Rebuplican masu martaba manufofin kasashen waje, don ganawa da sabon sarki Salman na Sa'udiyya. Wannan ziyarar dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan rasuwar marigayi sarki Abdullah. Sannan kuma ziyarar ta zo ne lokacin da rikicin kasar Yemen ke kara kazanta.

Kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya labarta, ziyarar tawagar Amirkar ta gaggawa, na da nufin inganta dankon zumunta sama da manufofin tsaron yankin. Saudiyya dai ta kasance daya daga cikin kasashen da ke goyon bayan manufofin kasar Amirka na yin Allah wadi da ayyukan kungiyar nan ta IS mai da'awar kafa daular Islama, kungiyar da a yanzu take tsaurara hare-hare a kasashen Iraqi da kuma Siriya