1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari kan 'yan takarar neman shugabancin Najeriya

Ubale Musa daga AbujaDecember 11, 2014

Masu ruwa da tsaki da harkokin siyasar Tarayyar Najeriya sun fara maida martani ga bullar manyan 'yan takara biyu da ke shirin jagorantar fagen siyasar kasar a zabukan da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1E2uU

Duk da cewar dai hankali na kwance suka kai ga murkushe kowa tare da karbar tutar jan ragamar jam'iyyar a bangare na magoya baya na shugaban kasar, da damansu dai sun share tsawon wunin wannan Alhamis suna kallo daga nesa ko wane ne za su ja da shi a kokarin su na tabbatar da shekaru 60 na mulkin PDP a kasar. A wannan karo dai ana kallon bullar jagoran sauyin da ke zaman dan siyasa mafi farin jini tsakanin talakawan kasar a matsayin babban kalubale ga jam'iyyar da har yanzu ke da tsohon bashi a idanun talakawa, sannan kuma ke fuskantar zargi na gazawa ciki da ma wajen kasar.

Buhari bai da ban tsoro

General a.D. Muhammad Buhari
Hoto: DW/N. Zango

Senata Saidu Umar Kumo dai na zaman daya a cikin shugabannin kungiyoyin tabbatar da zaben na Jonathan da ke cikin kasar ba adadi yanzu, kuma a fadarsa komai farin jinin na Buhari ba zai ba su tsoro ba.

"Mun shirya wa kowane irin yanayi na harkar zabe da siyasa, kuma muna ganin zai zama abun alfahari ga Najeriya da Afirka. Bamu shakkar APC kuma bamu shakkar Buhari, ai ba abu ba ne sabo."

Tsoro ga takara ta Buhari, ko kuma hanyar nasarar da ko makaho bai shakka dai, a wannan karon ko bayan farin jinin janar Buhari, akwai kuma batun cewar ita kanta APC da yake yi wa jagora na da karfin da ya zarci sa'a a cikin tarihi na adawa ta kasar.

Abun kuma da ya sa wasu ke tsoron yiwuwar barkewar rikici shigen na shekara ta 2011 da ya lamushe rayuka da daman gaske sakamakon boren talakawan da ke ganin an saba ga Buharin.

Mummunan yanayi

Dr Kole Shattima dai na zaman masanin harkokin siysar kasar ta Najeriya.

"Yadda mutane aka sake rarraba kansu bisa addini da siyasa da bangaranci, ga kuma rikicin Boko Haram da ake gani kamar gwamnati ce ke da hannu ko 'yan siyasa. Dole ne duk mai hankali ya dauka cewar yanayin da muke ciki ya fi muni fiye da 2011."

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar dukkansu 'yan jam'iyyar APCHoto: Atiku Media Office

Siyasar kudu da arewa da ma banbancin addini ne dai ya kai ga ta da hankali a tsakanin magoya bayan 'yan takarar da ke shirin sake gwajin kwarjini yanzu, bayan zaben shugaban kasar na watan Aprilun 2011. Siyasar kuma daga dukkan alamu har yanzu ke tsakar zuciya ta 'yan kasar da ruwan fatara da talauci ya kai wa iya wuya sannan kuma ke kallon na gazawa ga batun tsaro da tabbatar da zama na lafiyarsu.

To sai dai kuma a fadar Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali da ke zaman mashawarcin shugaban kasar na siyasa, wai tuni kan mage ya kai ga waje kuma tuni aka daina daukar ta zuwa ga farautar bera.

"Yanzu jama'armu na Najeriya ba za su yarda wani ya daura musu igiya ya rika jansu ba, domin yanzu suna da imani, kuma da ganewa, kuma sun gane masu kokarin raba kansu domin cimma buri na siyasa, kuma sun san in dare yayi, wanda ya neme ka da arziki shi ne naka."

Abun jira a gani dai na zaman nisan tsakar daren da ma alherin da ya boye a tsakanin 'yan kasar da suka dauki tsawon lokaci suna ta lalube.