1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta yi taron kolin 2016 a Warsaw

Yusuf BalaMay 22, 2015

A taron koli da NATO ta zauna a Satimban bara a Wales, shugabanninta sun amince da samar da kawancen soji da za su zama garkuwa ga kungiyar daga kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/1FVEf
Türkei - NATO Treffen mit dem ukrainischen Aussenminister Pavlo Klimkin
Mahalarta taron NATOHoto: NATO

Kungiyar tsaro ta NATO ta bayyana a ranar Jumma'a nan cewa za ta yi babban taron kolinta na gaba a birnin Warsaw a ranakun takwas zuwa tara ga watan Yuli na shekara mai zuwa, a zaman tattaunawar tinkarar kalubalen barazana da take fiskanta daga Rasha daga gabashi da barazanar masu jihadi daga kudanci.

Birnin na Warsaw da ke zama fadar gwamnatin kasar Poland shi ne a baya ya taba karbar bakuncin tattaunawar da ta kai ga samar da yarjejeniyar Warsaw da ke adawa da kawancen na NATO tsakanin kasashen Moscow da kawayenta daga gabashi wadanda suka ci gaba da wanzuwa har sai a lokacin faduwar Tarayyar Sobiyat a shekarar 1991.

A taron koli da kungiyar ta zauna a watan Satumban bara a birnin Wales, shugabannin kungiyar sun amince da samar da kawancen soji da zasu zama garkuwa daga gabashi yayin da kasar ta Rasha ke kara mara baya ga 'yan awaren gabashin Ukraine.