1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta tura karin sojoji da jiragen saman yaki gabacin Turai

April 16, 2014

Da ma tuni kasashen yankin Baltic hade da kasashen Poland da kuma Romaniya sun yi kira ga kungiyar kawance da ta tura dakaru yankin.

https://p.dw.com/p/1Bjei
Ostukraine Krise Rasmussen PK 16.04.2014 Brüssel
Hoto: Reuters

A dangane da rikicin kasar Ukaine, kungiyar kawance tsaro ta NATO ta ba da sanarwar kara yawan sojojinta a kasashe membobinta na gabacin Turai. A lokacin da yake magana bayan wani taro da jakadu 28 na kasashen membobin kungiyar ta NATO Babban sakataren kungiyar Anders Fogh Rasmussen ya ce a cikin kwanaki masu zuwa za a tura karin sojojin kasa da na ruwa da kuma na sama a wannan yanki. Wannan matakin na zuwa ne bayan kiran da kasashen yankin Baltic da Poland da kuma Romaniya suka yi. A kuma halin da ake ciki ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov wanda yanzu haka yake Vietnam inda daga nan zai zarce birnin Geneva don halartar wani taro kan rikicin na Ukraine, ya yi kira da a yi wa kundin tsarin mulkin Ukraine kwaskwarima don duba 'yanci da bukatun dukkan 'yan kasar. A ranar Alhamis ake gudanar da wani babban taro kan kasar ta Ukraine a Geneva.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu