1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ana zabe a inda ba a yi ba jiya

Ahmed SalisuMarch 29, 2015

Jama'a sun cigaba da kada kuri'unsu a yankunan da ba a samu kada kuri'a ba a ranar Asabar. Mazabu kimanin 300 ne dai aka gudanar da zabukan a ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/1EzFF
Wahl in Nigeria Wählerinnen in Jigawa
Hoto: DW/Z.Rabo

Labaran da ke shigo mana daga Kano na cewar ana yin zabe a wasu mazabu da ba kai ga yin zaben na shugaban kasa da na 'yan majalisu ba a jiya. Wakilinmu Nasir Salisu Zango ya ce zaben na gudana ba tare da an fuskanci wani kalubale ba. Nasiru din ya ce can a ofishin hukumar zaben mai zaman kanta da ke Kano din ana cigaba da tattara sakamako na zaben kafin daga bisani a kai ga bayyana abinda kowanne dan takara ya samu.

Wakilinmu da ke Abuja kuwa Uwais Abubakar Idris ya ce a Abuja ma zaben na gudan ba tare da fuskantar matsaloli ba sai dai ya ce a wasu mazabun ba a yin amfani da na'urar nan ta tantance mutum wato Card Reader. Can ma a arewa maso gabashin Najeriya zaben na cigaba da gudana ba tare wani korafi ba a wuraren da ake gudanarwa.

A kudu masu yammacin kasar kuwa kusan a iya cewa an kammala zaben ma don yanzu haka an yi nisa wajen tattara sakamakon. Masu aiko da rahotanni suka ce sakamakon ya fita a kananan hukumomi da dama kuma ma tuni har an fara mika su ga zauren tattara sakamako na wasu jihohin yankin.