1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na sa ran sako 'yan matan Chibok

Abdourahamane HassaneOctober 21, 2014

Ministan harkokin wajen Najeriyar Aminu Wali shi ne ya bayyana haka a birnin Berlin na Jamus a lokacin ganawarsa da takwaransa Frank Walter Steinmeier.

https://p.dw.com/p/1DZSE
Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Minisran ya bayyana cewar suna kyakyawan fatan cewar za a sako 'yan mata nan,'yan makaranta na garin Chibok sama da 200 waɗanda Ƙungiyar Boko Haram ke yin garkuwa da su. ''Zan iya cewar muna da ƙwarin gwiwa cewar mun kamo hanyar sakin waɗannan 'yan mata nan bada daɗewa ba, akwai nasarori da muke ganin an cimma a zahiri.''

A ranar jumma'ar da ta gabata ne rundunar sojojin Najeriyar ta ba da Sanarwa cewar ta cimma shirin tsagaita buɗe wuta da Ƙungiyar Boko Haram. Sai dai kuma duk da haka an ci gaba da ba da rahotannin kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashi na ƙasar da ke fama da tashin hankalin.