1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane miliyan 19 ba su san suna da aids ba

July 16, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa mutane miliyan 35 na dauke da Aids ko Sida a duniya . Sai dai fiye da rabinsu ba su san suna dauke da kwayar cutar HIV ba.

https://p.dw.com/p/1CeEG
Plakate - Deutsche Aidshilfe
Hoto: DAH

Jamiai daga wannan cibiya ta MDD na ganin cewa nan da shekarar 2030 zaa rage mace-mace ta sanadiyar cutar da sabbin masu kamuwa da ita da kashi casin cikin dari, duk kuwa da cewa a bara kadai ma an samu wadanda suka kamu da ita kimanin mutane miliyan biyu, adadin da ake kallon ya yi yawa.

Amma acewar Abdurrazaq Hamza jamii a cibiyar nazarin cutar ta HIV da maganinta a asibitin Malam Aminu Kano dake a jihar ta Kano Najeriya wannan adadi ai ya fi yawane akasashe masu tasowa da suke da karancin sani akanta.

''Kasashe masu tasowa yawanci anfi samun bullar sabuwar cutar idan ka kwatanta da kasashe da suka ci gaba wadanda tuntuni sun sha kan cutar inda kafin kaji bullar sabuwar cutar sai ka dade kana bincike akai tukuna''

AIDS Kampagne in Pakistan
Hoto: DW/D. Baber

A baya dai wannan cibiya ta MDD ta fito da wani tsari na ganin dukkanin masu dauke da wannan cuta suna samun kulawar da ta dace nan da shekarar 2015, amma a shekarar bara masu dauke da wannan cuta miliyan 12.9ne ke shan magani miliyan 22 suna jira. Amma acewar mai magana da yawun wannan cibiya ta MDD Mariangela Simao ya zuwa yanzu masu cutar na samun kulawa musamman Afrika inda cutar tafi kamari.

''Tace akwai mutanen da aka gwadasu aka gano suna dauke da kwayoyin wannan cuta kuma kashi casain daga cikin dari na wadannan mutane suna samun kulawa kan cutar ta HIV a yanzu haka''

Wasu masanan dai naganin cewa abune da zai yi wuya a kawar da cuatar baki daya, amma acewar Abdurrazaq Hamza kawar da ita abune mai yiwuwa idan har kowane mutum zai bada gudunmawa ba kawai a zurawa gwamnatoci idanuba.

Mosambik Schwierigkeiten mit HIV-Test Patienten Cabo Delgado
Hoto: DW/E. Silvestre

''Kwale-kwalene muke kai kuma yana cikin ruwa akwai kuma igiyar ruwa wacce ka iya haifar da hadari wanda zai iya shafar kowa saboda haka kowa sai ya bada tasa gudunmawar malaman mu ne su fadakar da magoya bayansu shugabanni na unguwanni da gidaje kowa ya sani wannan cuta akwaita saboda haka kowa sai ya tashi yaje gwaji wanda ke da ita ya yi kokarin kare dan uwansa''

Tuni dai wasu gwamnatocin da kungiyoyin kasa da kasa suka himmatu wajen samar da cibiyoyin gwajin saura da me kowane mutum ya tashi wajen sanin matsayinsa a dangane da cutar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita : Suleiman Babayo