1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140710 Megacitys Jakarta LANG

January 21, 2011

Babban birnin na ƙasar Indonesiya dake a jerin manyan-manyan biranen duniya da ake wa laƙabi da Megacities, ya ƙunshi mutane daga ko wane sashe na al'umar ƙasar.

https://p.dw.com/p/ztxR
Cunƙoson ababan hawa a JakartaHoto: AP

A cikin shirin dake zama ci-gaba na salsalar shirye-shiryenmu akan manyan biranen duniya da akewa laƙabi da Mega Cities, za mu leƙa birnin Jakarta ne na ƙasar Indonesiya. Kimanin mutane miliyan 20 ne ke zaune a wannan birni wanda ke bunƙasa a kullum kuma ke zama cibiyar harkokin kasuwanci. A tsakiyar birnin kaɗai an ƙiyasce cewa mutane miliyan 10 ne ke zaune. Ayu Utami na ɗaya daga cikinsu. Ayu shahararriyar ‘yar jarida kuma marubuciya tana wallafa littattafai akan birnin na Jakarta. Akan haka wakiliyar DW Edith Koesoe-Mawiria ta kai mata ziyara a Jakarta, inda ta zanta da ita yayin balaguron da suka yi a cikin birnin.

Ita dai Ayu Utami sananniyar ‘yar jarida kuma marubuciya ta ƙasar Indonesiya, a rubuce-rubucenta ta fi mayar da hankali kan babban birnin ƙasar wato Jakarta wanda ke a jerin manyan biranen duniya da ake wa laƙabi da Mega Cities. Tana bayani game da yanayin birnin mai ban al'ajabi musamman zamantakewa tsakanin talaka da mai kuɗi, halayya ta gari da ta banza. Ta dai shahara ne sakamakon littafinta mai suna Saman wanda ya samu karɓuwa a ƙasar ta Indonesiya. An fassara wannan littafi a cikin harsuna fiye da 30 ciki har da Jamusanci. Ta bayyana birnin da cewa ba ya fara'a ga masu ƙaramin ƙarfi.

Rubuce-rubucen waƙoƙi kan bango

Yayin da suke tsaye a wata tashar jiragen ƙasa dake tsakiyar birnin na Jakarta Ayu Utami ta kankare wata takarda daga wani bango wadda akanta aka rubuta wata waƙa da wani mai bin diddigin al'adun Indonesiya Gunawan Mohammad ya wallafa. Ayu dai ta yi aiki tare da Gunawa a lokuta da dama. Waƙar na bayani game da zamantakewa tsakanin al'ummomi daban daban a Jakarta. Mutane kimanin dubu 300 daga ko-ina suke kwarara birnin a kowace shekara. To amma birnin ba ya sauya su, su kuma ba sa sauya shi, domin ɗaukacinsu suna zuwa ne saboda aiki kaɗai. Suna barin al'adunsu na gargajiya a gida domin a gare su birnin mai ƙunshe da harsuna da al'adu bila-adadin, ba zai taɓa zama musu gida ba.

Jakarta Literatur der Megacities
Shahararriyar mawallafiya Ayu UtamiHoto: DW

Ayu Utami kamar da yawa daga cikin mazauna Jakarta, ba a birnin aka haife ta ba. Tun tana ƙarama iyayenta suka yi ƙaura daga Bogor zuwa babban birnin na Indonesiya. Ko da yake daga cikin harsuna fiye da 50 da ake amfani da su a Jakarta babu Jamusanci a ciki, amma Ayu ta ɗan iya wannan harshe, a saboda haka ta karanta wani sashe na littafinta Saman da aka fassara da Jamusanci, da wannan harshe.

“Ya kalle ni. A wannan karon ya kalle ni cikin idanu na, ya zauna kusa da Rosano. Wannan wata gajeriyar hulɗa ce. Sai ka ce yana jin kunya, amma a lokaci ɗaya ya nuna isa. Ya juya ya kalli kwano na, sai ya ce: Amma abinci da kika ci ba yawa. Yayi murmushi.”

Littafin Saman ya samu lambar yabo ta majalisar 'yan fasaha

Wannan dai wata al'amara ce game da tarihin wani Fasto na majami'ar Katholika wanda ke taimakawa talakawa. Da ya fara wata soyayya sai yayi watsi da aikin coci. Littafin na Saman ya kuma ƙunshi tarihin wasu mata waɗanda suka so yin hannun riga da wasu al'adun gargajiya. A shekarar 1998 majalisar masu fasaha ta birnin Jakarta ta bawa wannan littafi lambar yabo ta littafi mafi daraja a Indonesiya. Yanzu haka Ayu Utami memba ce a wannan majalisa.

“A bara mun mayar da hankali kan birane. Kwamitoci da ƙungiyoyi da dama sun yi aiki kan wannan batu. Kwamitin marubuta adabi da kwamitin masu fasaha sun ƙirƙiro da wani shiri na bai ɗaya, wanda ya tanadi kafa manyan alluna irin na talla, da za su ƙunshi rubuce-rubuce na shahararrun mawallafan ƙasar Indonesiya, a wurare da yawa na birnin Jakarta. Burin da aka sa gaba na wannan aikin shi ne yadda za a fid da fasahohi da al'adu daga gidajen ajiye kayan tarihi zuwa ga bainar jama'a, wato zane-zane akan bango su zama wani ɓangare na rayauwar yau da kullum.”

Megacity Jakarta
Jakarta dai birne ne mai cike da ababe iri dabam-dabamHoto: AP

Gabatar da adabi da fasahohi kai tsaye ga jama'a a ko-ina a matsayin ɓangare na rayuwar amma ba a ƙargame su a cikin gidaje ba. Yayin balaguro neman wasu zane-zane akan bango, Ayu da wakiliyar DW sun isa wani wuri ƙarƙashin wata gada, amma maimakon sun sauka daga mota sai Ayu ta ce a ci-gaba da tafiya. Inda suka ci karo da wasu maza suna wasan karta, ɗaukacinsu dai ‘yan acaɓa ne da ‘yan tireda. Sun kan haɗu su yi wasa ko su huta. Akwai kuma masu zaman kashe wando a cikinsu. A tsakiyasu akwai wani bangon kankare wanda akansa aka liƙa ɗaya daya cikin zane-zanen da suka fi burge Ayu Utami. A halin da ake ciki birnin Jakarta ya cika da zane-zane na nuna fushi da kuma rubuce ruibuce na adabi. Suna dai bayanai game da abubuwan da suka ɗaukar hankalin mazauna birnin wato kamar adabin Ayu Utami.

“Ba na rubutu game da kyaun birnin na Jakarta. Na fi mayar da hankali kan yadda babban birnin ke canzawa. Manyan birane na Mega Cities kamar Jakarta, New York, Tokyo ko Berlin suna cike da ababai na al'ajabi. Waɗannan ababan na fitowa ne daga ɗan Adam amma ba daga birnin ba.”

Birnin Jakarta na canzawa a kullum

Masu iya magana kan ce mutum shi ne gari amma ba gidaje ba. A cikin wani rubutu mai taken “Trotoa”, Ayu ta yi bayani game da hanyoyin da ake keɓewa mutane a gefen tituna a Jakarta da kuma muhimmancinsu. Ta yi magana da wani tattaki da ta yi cikin dare da wani mai shirya fina-finai na ƙasar Netherlands. Da suka shagala da hira kan wani fim da ba ta jima da gani ba, sai abokin tafiyarta ya faɗa wani ramin kan hanya. Maimakon yi masa jaje sai ta fusata.

“Ba a gina hanyoyin nan da kyau ga jama'a ba, duk da cewa an yi gyare gyare a wasu wurare na birnin. Amma wata matsalar kuma ita ce, mutanen da ake abin domin su ba sa ɗaukanshi da muhimmanci. Ba sa daraja kayakan gwamnati. Ga misali a wuraren da aka gina hanyoyi masu faɗi ga jama'a, za ka tarar mutane na amfani da su a matsayin wuraren saye da sayarwa. Ka ga ba za ka iya bin wannan hanya cikin sauƙi ba. A wasu lokutan wasu ‘yan banga ke iko da wuraren, inda suke karɓan kuɗaɗe daga wurin jama'a, musamman idan hukuma ta yi rauni.”

Megacity Jakarta
Kowa harkar gabansa ya sha masa kaiHoto: AP

Ko da yake Jakarta birni ne da mutum zai iya faɗuwa saboda ramuka a hanyoyi, amma dole sai an yi hattara saboda rashin fitulu masu haskaka hanya, inji Ayu sannan sai ta ƙara da cewa.

“Ba a yiwa talakawa adalci a Jakarta. Ana nunawa talakawa wariya a birnin. Hukumar birnin ta na yawaita sa ido akan talakawa domin tabbatar da bin doka da oda. Amma waɗannan dokoki ba sa taimakawa talakawan wajen tafiyar da rayuwarsu. Hasali ma dokokin ke sa talakawa za ma masu aikata laifuka.”

Duk wani mataki na kyautata rayuwa a wannan babban birni ana yin sa ne domin masu kuɗi. Bankaɗo irin waɗannan batutuwa na rashin adalci sun fi samun karɓuwa a aikace aikacen Ayu Utami.

Mawallafa: Edith Koesoe-Mawiria/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu