1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane masu fama da nakasa

August 11, 2010

Mutane masu fama da nakasa sukan fuskanci wariya a rayuwarsu ta yau da kullum.

https://p.dw.com/p/OiFR
Hoto: LAIF
Saboda irin nakasar da suke fama da ita, mutane kan yi watsi da su ta hanyar nuna musu wariya. Ka samu sanin ɗaya daga cikinsu, domin sanin irin kalubale da suke fuskanta.

Kashi goma na yawan al'ummar duniya ne ke rayuwa da matsalar nakasa. Ana iya ganin hakan a bayyane a biranen Afirka, yadda ake nuna halin rashin kulawa ga makafi da guragu, da ke ƙoƙarin samun abin dogaro ta hanyar barace-barace. Wasu iyalan ma kan kulle 'yan uwansu naƙasassu akan cewar abin kunya ne a gare su, ko kuma tsinannu ne.

Akwai dokoki masu yawa da ke kare 'yancin nakasassu. Sai dai duk da haka mafi yawa daga cikinsu na ci gaba da fuskantar shinge daga al'umma. Suna fuskantar wariya a fannonin rayuwa, tattali, al'adu da kuma 'yancin shiga harkokin siyasa ko tofa albarkacin bakinsu.

Wannan sabon wasan kwaikwayo shinrin ji ka ƙarun zai kai masu sauraro zuwa maganye, wani gari dake surƙuƙin hamadar Afirka. Za ku ji labarin Habu, wanda cikin gajeren lokaci ya kasance nakasasshe, wanda ya tilasta masa fuskantar sabbin kalubalen rayuwa. Ka yi nasarin sakonsa mutane duk ɗaya suke da nakasa ko babu. Kowa yana da fatan cimma buri a rayuwa.

Ana iya sauraron shirin Ji Ka ƙaru a harsuna shida: Turanci, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portugues da Amharik. Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ke tallafawa shirin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar