1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawuyacin hali a Mubi sakamakon Boko Haram

Abdul-Raheem HassanOctober 30, 2014

Rahotanni daga Mubi na nuni da cewar 'yan kungiyar Boko Haram sun kwace madafan ikon garin, inda tuni suka kafa tutarsu a kofar sarki tare da rusa ofisoshin jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/1De9x
Nigeria Kano Bombenanschlag
Hoto: Reuters

Da sanyin safiyar Alhamis ce dai 'yan kungiyar ta Boko Haram suka afkawa garin na Mubi, inda suke cin karensu babu babbaka. Kafin shiga garin na Mubi dai, sun yada zango a garuruwan Uba da kuma Mararaba-Mubi da ke Karamar Hukumar Hong, inda suka yi da musayar wuta da jami'an tsaro, tare da fatattakar mazauna garuruwan.

Adaidai lokacin da suke kokarin kafa tutarsu a tsakiyar garin na Mubi ne dai wakilimmu a Yola ya samu hira da wani wanda yayi karo da su. Ganau din ya shaida masa yadda suka kamashi kana suka sakeshi bayan ya yi kalmar shahada. Acewarsa dai 'yan Boko Haram din sun ce kada mutane su gudu don basu da niyyar taba kowa. Amma kowa ya razana, ganin cewar jami'an tsaro ma sun tsere daga garin.

Rahotanni sunce yanzu haka dai 'yan bindigar sun kewaye garin na Mubi, tare da kafa tutarsu a kofar sarki da rusa dukkan ofisoshin jami'an tsaro da ke Mubin.

Gidan babban hafsan tsaron Najeriya Alex Bade na cikin Karamar Hukumar ta Mubi ne, inda yanzu Boko Haram ke ikirarin kasancewa a karkashinsu. Mazauna yankunan arewacin Adamawan dai na ci-gaba da tserewa domin tsira da rayukansu daga hare haren 'yan bindigar.