1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mauritaniya ta ɗauki matakan kariya kan Ebola

October 25, 2014

Hukumomin ƙasar Mauritaniya sun tsaurara matakan bincike kan iyakokinsu,bayan da aka samu ɓullar cutar Ebola a ƙasar Mali mai makwaɓtaka da wannan ƙasa.

https://p.dw.com/p/1DcCX
Hoto: Reuters/J. Penney

Binciken dai ya fi ƙarfi musamman ma a birnin Kayes da ke a matsayin wata mahaɗar harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. A cewar Ahmedou Ould Jelvoune ministan kiwon lafiyar ƙasar ta Mauritaniya, tuni suka bayar da umarni a ko'ina na ɗaukan matakkan rigakafi ganin yadda ƙasar ke da iyaka mai tsawon aƙalla km 2.200 tsakanin ta da ƙasar ta Mali. Yarinyar dai 'yar shekara biyu da aka gano cutar ta Ebola a gareta a ƙasar ta Mali ta rasu, sai dai kuma hukumomin ƙasar sun samu tattara aƙalla mutane 50 da ake ganin sun yi mu'amula da ita ko kakarta, inda suke ƙarƙashin kulawar likitoci a halin yanzu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane