1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080811 USA Finanzen

August 9, 2011

Farashin hannayen jari ya faɗi warwas, tun abin da ya kama daga Japan har ya zuwa New Zealand

https://p.dw.com/p/12DJU
Hoto: dapd

 Ana fama da hali na rashin sanin tabbas a kasuwannin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa. A daidai lokacin da ake kai ruwa-rana dangane da matsalar bashin dake addabar ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai sai kuma gashi an naƙasa matsayin Amirka na ikon karɓar basussuka. A dai halin da ake ciki yanzu an ɗokata a ga yadda al'amura zasu kaya bayan an buɗe kasuwar hannayen jari na ƙasar Amirka a ranar litinin.

Aƙalla dai ci gaba da tabbatar da Tim Geither kan muƙaminsa na sakataren baitul-malin ƙasar Amirka ya taimaka aka samu daidaituwar al'amura a kasuwannin cinikin hannayen jari a sassa daban-daban na duniya. Wannan maganar ma dai ita ce ta mamaye kanun rahotannin gidajen telebijin ƙasar Amirka a yammacin jiya lahadi. Tim Geither dai shi ne wani babban jami'i ɗaya ƙwal da ya rage a tawagar tattalin arziƙin shugaba Barack Obama, wanda tun da farkon fari ake damawa da shi. Yana daga cikin masu sukan lamirin kafar nan ta Standard and Poor's mai ƙayyade matsayin karfin tattalin arziƙin ƙasa da ikonta na karɓar bashi ya kuma zargeta da caɓa kurakurai a lissafinta. David Beers daga kafar ta S&P a taƙaice, ko da yake ya amince da maganar caɓa kurakuran, amma yayi fatali da sukan lamirinta da ake yi:

Frankfurt Börse Crash Kursverluste Finanzkrise Handelsschranken
Hoto: dapd
:"Babu wani canjin da aka samu dangane da sakamakon da muka cimma, hatta bayan da muga shigar da lissafin muka kuma tattauna da ma'aikatar kuɗi. Duk ma da daidaituwar da aka cimma a majalisar dokoki dangane da ƙayyade yawan basussukan a makon da ya gabata, bashin dake kan gwamnatin Amirka zai ci gaba da ƙaruwa, mai yiwuwa ma dangane da shekaru goma masu zuwa."

Amirkawa dai sun zura na mujiya domin ganin yadda al'amura zasu kaya a kasuwannin hannayen jari a ƙasashen Larabawa da Isra'ila kama daga ƙarshen mako zuwa yau litinin. An samu faɗuwar farashin hannayen jarin a waɗannan kasuwanni da misalin kashi huɗu zuwa kashi shida cikin ɗari. An fuskanci irin wannan matsalar a kasuwannin Asiya. A sakamakon haka Marc Sandy, babban jami'in tattalin arziƙi na cibiyar bashin ƙwai akan al'amuran cinikin hannayen jari Moody's Analysis ke kyautata zaton fuskantar koma baya a kasuwar hannayen jari ta Wallstreet. Sai dai kuma Alison Kosik, mai ake wa da tashar CNN da rahotanni akan al'amuran kuɗi ta ce mai yiwuwa a samu wani ci gaban na dabam tana mai yin nuni da koma bayan kashi goma cikin ɗarin da aka fuskanta a kasuwar ta Wallstreet a cikin makonni biyun da suka wuce.

:"Dangane da Wallstreet dai tuni ta faru ta ƙare kuwa babu ragowar fargaba ga al'amuranta. A yanzu muna iya fuskantar wata alƙibla dabam. Kuma hakan ka iya zama alheri bisa manufa."

Amma a nasa ɓangaren Muhammed El-Erian, shugaban kafar zuba jari ta Pimco ya ce a ƙashin gaskiya yana cikin hali na ɗardar kuma bai san ainihin alƙiblar da zai fuskanta ba:

Aktienkurs DAX Börse Crash Kursverluste Finanzkrise Schuldenkrise Asienkrise Wirtschaft
Hoto: picture alliance/dpa
:"Abokan aikina na tattaunawa da masu ajiya tare da tambayarsu abin da suke ƙaunar yi. Muna da shawara guda biyu da zamu iya bayarwa. Da farko muna iya riƙe ajiyar mu kuma canza alƙibla, sannan na biyu muna iya sayar da takardun ajiyar."

A dai halin da ake ciki yanzu ana fuskantar wata matsala ce inda mutane ba su amince da al'amuran kasuwa ba suke kuma ɗariɗari da manufofin baitulmalin ƙasa ta la'akari da yadda martabar Amirka ta zube dangane da ikonta na karɓar basussuka.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar