1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar sojojin kasar Faransa a Bangui

February 25, 2014

Firaministan Faransa Jean-Marc Ayrault ya yarda cewa sojojin kasarsa na fuskantar matsala a kokarin da suke yi na shiga tsakanin Musulmai da Kiritoci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/1BFIn
Afrika Gewalt in Bangui 29.01.2014
Hoto: AFP/Getty Images

Jean Marc-Ayrault ya yi wannan bayanin ne a zauren majalisar dokoki da ke birnin Paris, inda ake tafka muhawara a kan wajibcin kara sojojin Faransa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin mayar da doka da oda a kasar. Shi dai firamiyan ya nunar da cewa ko da shi ke sannau a kan hankali an fara gano bakin zaren warware rikicin, amma kuma akwai bukatar ci-gaba da kiyaye zaman lafiya har bayan zaben da za a gudanar a watan Fabreru na shekara mai zuwa. Ana sa ran daukacin 'yan majalisan na Faransa za su amince da karin sojojin kasarsu a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Firaministan na Faransa ya nuna wajibcin tura sojojin kiyaye zaman lafiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, idan dai ana so a raba Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da tashin hankalin da take fama da shi yanzu haka. Saboda haka ne ya nemi mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su duba rahoton da babban sakataren majalisar zai mika musu kan rikicin addinin na Afirka ta Tsakiya da idanun basira.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman

AFP