1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa ne amma suna da faɗa a ji – Haƙƙin Yara a Afirka

March 30, 2010
https://p.dw.com/p/LYje
Hoto: LAI F


Yara a Afirka kan fuskanci wahala a rayuwa. Akwai masu tafiya mai nisan gaske zuwa makaranta ko kuma zama a yankin rikici – Shirin Ji Ka Ƙaru zai kawo muku wasu misalai na ƙalubalen da yara ke fuskanta da kuma haƙƙinsu a nahiyar Afirka.


A yayinda a nahiyar Turai yara ke da abin wasa iri-iri, a nahiyar Afirka galibi yara kan shagala ne da aikace-aikace. A karkara dubban ɗaruruwan yara kan je makaranta da safe sannan su taimaka wa iyayensu a gona da maraice. Wasu yaran ma su ne ke ɗaukar nauyin kulawa da kansu tun suna ƙanana saboda rashin wadatar iyayensu.

Sau tari yara kan sha fama da wahala a rayuwa a Afirka. Nahiyar ta fi kowace yawan mace-macen yaran da suka gaza shekaru biyar da haifuwa. A wani lokacin yaran na zama ne a wuraren da ake fama da rikici da rashin tsaro. A baya ga haka da wuya su samu nagartaccen ilimi kamar takwarorinsu a Asiya ko Amurka ko kuma Turai.

Shirin Ji Ka Ƙaru zai kawo muku labarin wasu daga cikin waɗannan ƙananan gwarzayen Afirka. Maganar ba ta tsaya akan gwagwarmayarsu ne kawai ba. Kazalika ta haɗa da mutanen dake fafutukar tabbatar da haƙƙin yara da kawo canji a rayuwarsu. Shirin har ila yau zai duba irin ci gaban da aka samu. Misali akwai majalisun wakilai na yara dake fafutukar tabbatar da haƙƙin yara a Nijeriya.