1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu bore a Ukraine sun ce za su dauki matakan kare kansu.

April 20, 2014

Masu hamayya da hukumomin Ukraine, a garin Bilbasivka da ke gabacin kasar sun ce za su nemi makamman kare kansu daga masu kai musu hari.

https://p.dw.com/p/1BlSF
Hoto: DW/R. Goncharenko

Al'amura sun fara daukan wani sabon salo a kasar Ukraine, bayan da wasu motoci guda hudu cike da mutane suka zo a guje kuma mutanan dake ciki, suka buda wuta kan masu adawa da gwamnatin kasar dake garin Bilbasivka a gabacin kasar ta Ukraine, inda harin yayi sanadiyar mutuwar mutane uku daga cikin masu goyon bayan Rasha.

A cewar Evgueni Bondarenko, wani dattijo dan shekaru 62 da haihuwa, daya daga cikin masu goyon bayan kasar ta Rasha da ke gabacin Ukraine, da kuma ya gane ma idanunsa abun da ya wakana, ya ce mutanen dai ba sojojin Ukraine ba ne, domin basu da kayan soja a jikinsu, inda yace kawai 'yan ta'adda ne na Pravy Sektor wasu 'yan gani kashenin kasar ta Ukraine suka kawo wannan hari.

Inda ya kara da cewa tun da abun ya zamana haka, to dole su ma su nemi makamman kare kansu, kuma ba za su taba yarda da kowa ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal