1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar za ta ci gaba da yaƙar 'yan ta'adda

Ahmed SalisuOctober 25, 2014

Gwamnatin Masar ta ce akwai hannun wasu mutane daga wajen ƙasar a harin nan da aka kai yankin Sinai kuma ta daura damar yaƙarsu.

https://p.dw.com/p/1Dc6Y
Ägypten Präsident Abdel-Fattah al-Sisi Vereidigung 08.06.2014 QUALITÄT
Hoto: Reuters

Shugaban ƙasar Abdel-Fattah al-Sissi ne ya bayyana hakan inda ya ke cewar wasu ne daga waje ne ke fafutukar ganin sun karya kashin bayan Masar, to sai dai bai yi ƙarin haske game da wanda ya ke zargi da kai harin ba. Al-Sisi ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta daƙile dukkannin wani yunƙuri na 'yan ta'adda a duka sassan kasar ko da dai a cewarsa hakan zai ɗau tsawon lokaci amma ya ce ba za su gajiya ba sai sun kai ga ci.

Gwamnatin Masar ɗin dai ta sanya dokar-ta-ɓaci a yankin na Sinai sannan ta ware kwanaki uku domin yin zaman makoki na waɗanda suka rasu sakamakon harin da aka kai.