1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da samun hare-hare a Baga

Umaru AliyuJanuary 9, 2015

A Najeriya ana maida martani a kan mumunan harin da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Baga, inda suka kashe mutane masu yawa

https://p.dw.com/p/1EHx1
Nigeria Baga Kämpfe mit Boko Haram 21.04.2013
Hoto: picture alliance/AP Photo

Karo na biyu kenan a cikin mako guda ana kai hari a kan garin na Baga da ke jihar Borno, wanda ke da muhimmancin saboda kasancewarsa kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Chadi, kuma wanda kafin wannan hari akewa kallon tudun na tsira saboda hedikwatar sojojin kasa da kasa da ke yankin.

Rahotani na gani da ido sun bayyana yadda aka kone mafi yawan gidajen da ke garin na Baga abinda ya maida shi tamkar kufai da aka dade babu alamun rai a cikinsa. Wannan ya tilastawa dubban jama'ar da suka samu arcewa gudun hijira tare da shiga mawuyacin hali. Sanata Maina Ma'aji Lawan dan majalisar dattawa ne da ke wakiltar yankin, ya bayyana takiacin abinda ya faru.

‘'Wannan abu ba sau daya ba sau biyu yake faruwa ba shi yasa na farko a yanzu irin halin tashin hankali ya sanya aka wargaje daga garin kuma ba Baga ba kadai a ko ina da irin wannan abu ya faru haka abin ke faruwa, shi yasa taimako muke nema a yanzu daga gwamnati da ma sauran jama'a saboda mumunan hali na ‘yan gudun hijira da muka shiga a yanzu''.

Abinda ke daga hankali shine yadda sojojin Najeriya suka bari aka kai wannan harin ba tare da daukar wani mataki na kare garin ba, bayan fuskantar irin wannan a cikin makon nan. To ko wace illa hali na gaza kare wasu daga cikin hare-haren ke dashi ga sojojin Najeriyar? Mallam Hussaini Mongunu masani a fanin tsaro a Najeriyar.

Alhaji Kashim Shettima
Gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim ShettimaHoto: DW/U. Musa

‘'Idon duniya a yanzu ba a kallon sojojin Najeriya da daraja kuma ba daukarsu suna da gaskiya, in ka duba ko jiragen yaki da ake son a saye daga Israila ai Amurka ta hana saboda tana zargin sojojin Najeriya suna da hannu a wannan rikicin. Saboda haka a yanzu sojan Najeriya bashi da wata martaba a idon duniya''.

Amma ga Mr Mike Omeri shugaban cibiyar samar da bayanai a kan harkokin tsaron Najeriyar yace a gaskiya suna kokari kuma ma dai suna neman karin goyon baya.

Amma ga Sanata Kabiru Gaya na majalisar dattawan Najeriya na mai kalubalantar shin wane hadin kai ne gwamnatin Najeriya ke bukata da bata samu ba ya zuwa yanzu?

Nigeria Baga 2013
Jami'an tsaro a jihar BornoHoto: Pius Utomi/AFP/Getty Images

‘'Goyon bayan duk da suke nema ai an basu musamman ma dai mu ‘yan majalisar tarayyar da sauran ‘yan Najeriya. Sanatocinmu musamman masu kishi daga yankin arewa da na jihohin Borno Yobe da Adamawa mun ta kira a yi kokari a kashe wutan nan aka yi biris. To sojan Najeriya ba haka ya kamata ya zama ba, ya kamata ya tsaya ya kare kasarsa, kuma gwamnatin hakkinta ne ta kashe wannan wutar''.

Kwararru na masu bayyana tsoron abinda ka iya biyo bayan kame garin na Baga a ci gaba da fsukantar matsala ta rashin tsaro da ke adabar Najeriyar.