1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan hadin kai a Palasdinu

Mahmud Yaya AzareApril 24, 2014

Kungiyoyin Fatah da Hamas na Palalsdinu sun kulla yarjejeniyar sulhun da za ta kai su ga kafa gwamnatin hadaka nan da watanni shida masu zuwa.

https://p.dw.com/p/1Bo7n
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan da suka kwashe kusan shekaru bakwai suna zaman 'yan marina kwatsam sai kungiyoyin biyu suka ba da sanarwar kulla yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa a tsakaninsu, lamarin da ya jawo martini daga palasdinawan kansu dama kasashe makwabta. Baki dayan al'ummar palasdinawa dai sun nuna matukar farin cikinsu da wannan yarjejeniya ko da yake wasu sun nuna taka tsantsan kan nasarar aiwatar da yarjejeniyar sulhun a daidai lokacin da kasashen dake da ruwa da tsaki a kan tabbatar da zaman lafiya tsakanin kasashen palasdinu da Isra'ila ke nuna damuwa kan wannna abin da palalsdinawan ke rangada guda a kansa.

Yarjejeniya mai matukar tarihi

Da yake bayyana ra'ayinsa kan batun, jagoran palasdinawan yankin Zirin Gaza Isma'il Haniyya ya ce wannan yarjejeniyar ta tarihi ce.

Gaza Hamas Fatah Palästinenser Treffen 23.04.2014
Shugabannin kungiyoyin Hamas ta Fatah na nuna farin cikinsuHoto: AFP/Getty Images

'Wannan abin albishir ne da muke isarwa il'lahirin palasdinawan dake ciki dama wadanda ke waste a uwa duniya. Wato kawo karshen zaman doya da manjan dake tsakaninmu."

Shima wakilin kungiyar Fatah Azzam Al-ahmad ya nuna fatan samun dorewar wannan sasantawar don tunkarar kalubalen mayayar da Isra'ila ke wa yankin da yunkurinta na yin karfa karfa a birnin Qudus mai dimbin tarihi.

"Da yardar mai duka wannan shine danba na wanzuwar hadewa da aiki tare tsakanin il'lahirin bangarorin Palasdinawa dake da banbancin ra'ayoyin siyasa."

Dandazon palalsdinawan da suka halacci farfajiyar zauren da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar sasantawar sun nuna farincikinsu ko da yake wasunsu da sukai ajiyar zuciya sunce ba girin girin ba dai tayi mai::

"An dade ana ruwa kasa na shanyewa. Sau nawa suke cewa sun sasanta kana su sake yin baram baram? Ni aganina sasantawa ba maganar fatar baki bace .Mudai mugani a kasa."

Ra'ayin makwabtan Palasdinu

Kasar Masar dake sa-in-sa da kungiyar Hamas dake dasawa da 'yan uwa musulmi wacce kuma take ci gaba da rufe mashigar Rafah da mazauna yankin Gaza ke tsallakawa zuwa ketare ta bakin ministan harkokin wajanta Nabeel Fahmi cewa ta yi ta na fatan wannan yarjejeniya za ta karawa palasdinawa karfin gwiwar ci gaba da gwagwarmayarsu ta samun kafuwar kasarsu mai cin gashin kai, kamar yadda itama kasar Jodan da Majalisar Dinkin Duniya ta dankawa hakkin lura da wurare masu tsarki na palasdinawa dake karkashin mamayar Isra'ila ta ce yarjejeniyar wani kwakkwaran naushi ne a hancin makiyan kafuwar kasar Palasdinu.

Benjamin Netanjahu
Firaminstan Isra'ila Benjamin NetanjahuHoto: picture-alliance/dpa

Ita kuwa Isra'ila da ta fara maida martini da kai hare-hare kan yankin Gaza da yakai ga jikkata mutane shida ta kara da yin tofin Allah tsine ga yarjejeniyar kamar yadda Firaministan kasar Benjamin Natanyaho ke cewa...

" Maimakon hukumar palasdinawa ta dukufa wajen samar da zaman lafiya tsakaninta da Isra'ila sai ta sasanta da kungiyar 'yan ta'adda ta Hamas. Zabi daya garesu kodai su sasanta da Hamas su bata damu, ko kuma su sasanta damu a samu zaman lafiya amma taura biyu bata taunuwa a baki lokaci guda."

Maawallafi: Mahmud Yaya Azare

Edita: Pinado Abdu Waba/ LMJ