1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maradona na ci gaba da daukan hankali

June 2, 2014

Kwallon da dan wasan na kasar Argentina, Diego Maradona ya jefa a ragar Ingila a wasan cin kofin duniya a 1986 na ci gaba da daukan hankali.

https://p.dw.com/p/1CAdz
Hoto: picture alliance/AFP

Kwallon da shahararren dan wasan kasar Argentina, Diego Armando Maradona ya jefa a ragar Ingila yayin wasan cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 1986, ya kasance a matsayin kwallon mafi daukaka na karnin da ya gabata.

Ranar 22 ga watanin Yunin shekarar 1986 yayin wasan kusa da na kusa da na karshe, a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar Mexico ta dauki nauyi aka kara wannan wasa tsakanin Argentina da Ingila.

Wasan da aka kara a filin wasa na Estadio Azteca da ke birnin Mexico City, ya zo bayan kammala yaki dakanin kasashen biyu bisa tsibirin Fulkland.

A wannan rana Diego Maradona ya kafa tarihi a kan hanyar lashe gasar na duniya da Mexico ta yi, domin mintoci 51 da fara wasan Maradona ya jefa kwallo mai cike da cece-kuce wajen amfani da hannu, kuma har yau tana cikin kwalloye mafiye janyo cece-kuce a tarihin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya. Amma mintoci uku kacal bayan haka kafin 'yan wasan Ingila su murmure sai Diego Maradona ya kafa wani tarihin.

Maradona ya dauki kwallon tun daga bangaren gidan Argentina yana yankiya da lelaya da keta tsakiyar 'yan Ingila inda ya wuce 'yan wasa da biyar kafin ya kai kan mai tsaron gida, sannan ya jefa kwallon cin ragar Ingila.

Wannan shi ya saka Maradona zama babban dan wasa a duniya, kuma ya tabbatar da hakan, yayin da kwallon farko bai kamata a kyale ba, wannan kwallon na biyu da Maradona ya jefa a ragar Ingila ya tabbatar da sahihancin kasancewar Maradona kwarzon 'yan wasa na duniya, an kara wasan a gaban kimanin 'yan kallo 114,580. An tashi wasan Argentina tana da ci 2 Ingila 1.

A shekara ta 2002 yayin zaben da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta gudanar aka zabi wannan kwallon da Maradona ya jefa a ragar Ingila, a matsayin kwallon mafi daukaka a aka jefa a raga a tsawon karni na 20 da ya gabata.

Kwallon farko mai cike da rudani Diego Maradona ya yi amfani da kalmar cewa "Hannu Ubangiji" saboda yadda ya yi amfani da hannun a fakaice wajen jefa kwallon, sai dai mai horas da 'yan wasan Ingila ya ce hannun sheda.

Argentina ta lashe wannan gasa na cin kofin kwallon kafa na duniya a Mexico, bayan doke kasar Jamus ta Yamma a lokacin gasar karshe.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal