1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fasinjojin jirgin Malesiya sun mutu

January 29, 2015

Hukumomin kasar Malesiya sun tabbatar da cewa baki dayan fasinjoji da ma'aikatan jirgin saman kasar mai lamba MH 370 da ya yi batan dabo sun mutu.

https://p.dw.com/p/1ET7C
Hoto: picture-alliance/dpa

Mahukuntan na Malesiya sun yanke shawarar bayyana mutuwarsu ne bayan cika kwanaki 327 da batan jirgin da ke dauke da mutane 239, inda suka ce iyalan mutanen da ke cikin wannan jirgi ka iya neman diyyar 'yan uwansu. A cewar shugaban sashen kula da zirga-zirgar jiragen saman 'yan kasuwa na kasar ta Malesiya Azharuddin Abdul Rahman da ya bada wannan sanarwa, yana fatan bada sanarwar fasinjojin da ma'aikatan jirgin mai lamba MH 370 su 239 sun mutu zai sanya dangin mutanen samun dukkan tallafin da suke bukata, kana ya kara tabbatar musu da cewa za su ci gaba da baiwa laluben jirgin muhimanci.

A ranar takwas ga watan Maris na shekara ta 2014 da ta gabata ne jirgin ya yi batan dabo a kan hanyarsa ta zuwa Beijing na kasar China, sa'a guda bayan da ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Kuala Lumpur na kasar ta Malesiya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba