1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malam Abdou Labo ya shiga hannu

August 25, 2014

Al'ummar Jamhuriyar Nijar sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da cafke ministan harkokin noman kasar Malam Abdou Labo.

https://p.dw.com/p/1D0fl
Hoto: DW

'Yan siyasa da kungiyoyin farar hula dama masana dokoki a Jamhuriyar Nijar sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da matakin da hukumomin shari'ar kasar suka dauka na cafke ministan harkokin noma na kasar Malam Abdou Labo tare da iza keyarsa zuwa gidan kaso na garin Say da ke da nisan kilomita 60 da Yamai babban birnin kasar a karshen makon da ya gabata.

Kamen na da alaka da cinikin jarirai

Da dama dai na ganin wannan kamu na Abdou Labo ba zai rasa nasaba da batun badakalar safarar jarirai da ake zargin wasu 'yan Nijar din sun yo daga Nijeriya ba. Kawo yanzu dai babu wani bayani da hukumomin shari'ar ko kuma lauyan Abdou Labon su ka yi dangane da dalilan kama shi da kuma zargin da ake yi masa. Sai dai ga dukkan alamu kamun nasa ba zai rasa nasaba da badakalar cinikin jarirai da ake zargin wasu 'yan Nijar din da yi ba, inda yanzu haka ake tsare da mutane sama da 20 a gidajen kurkuku ciki kuwa har da matar Malam Abdou Labon da ake zargi da mallakar jarirai da 'yan Nijar ke yi wa lakabi da cibiya na Imo.

Afrika Nigeria Impfung von Kindern
Safarar jarirai daga Najeriya zuwa NijarHoto: picture alliance/dpa

Da ta ke tsokaci a kan matakin kama ministan jam'iyyarsa ta CDS Rahama ta bakin kakakinta Malam Kabirou Adamou cewa ta yi batu ne na shari'a kuma matakin ba zai yi wani tasiri ba ga manufofin magoya bayansa dama goyan bayansu ga shugaban kasa da gwamnatinsa. Shima dai bangaren shugaban jam'iyyar CDS Rahama na kasa Alhaji Mahaman Usman cewa ya yi duk da matsalar da ke akwai tsakaninsa da bangaran Abdou Labo yana mai yi masa jaje dangane da abun da ya sameshi a cewar Malam Maman Nouroudine shugaban matasan jam'iyyar na kasa.

Matsayin shari'a kan kamen

Saidai yanzu haka 'yan Nijar da dama na ganin matakin kama ministan ba tare da cire masa rigar kariya ba, ya sabawa shari'a, sai dai Maitre Larwana masanin ilimin shari'a a Nijar din ya ce matakin bai sabawa ka'ida ba. Tuni dai wasu kungiyoyin farar hula da na kare hakkin dan Adam suka soma bayyana gamsuwarsu da matakin. Malam Nasirou Seidu shugaban kungiyar Muryar Talaka ma dai na da irin wanann ra'ayi. Abun jira a gani shine matakin da hukumomin shari'ar Jamhuriyar ta Nijar za su dauka kan makomar shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadou wanda shima ake zargi da hannunsa a cikin badakalar cinikin jariran.

Hama Amadou
Shugaban majalisar dokokin Nijar Hama AmadouHoto: DW/S. Boukari

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/ AH