1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Nijar ta yarda ta mika Hama Amadou

August 27, 2014

Kwamitin gudanarwar majalisar dokokin Nijar ya ba da izinin mika shugaban majalisar dokoki Malam Hama Amadou a gaban kuliya kan zarginsa da hannu a badakalar jarirai.

https://p.dw.com/p/1D2nG
Hajiya Hauwa Abdu
Hoto: DW/Mahamman Kanta

Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijar Honorable Mammadu Marte shi ne ya jagoranci zaman kwamitin gudanarwar bayan da shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadou wanda bisa al'ada ke jagorantar irin wannan zama ya kaurace wa taron. Haka nan kuma mambobin kwamitin bakwai daga cikin 11 wadanda duk 'yan bangaren da suka fi rinjaye ne suka halarci wannan taron. Honorable Ben Omar Muhamed mamba a wannan kwamiti ya yi mana karin haske a kan matakin nasu.

Ko da shi ke, tun ma kafin kwamitin gudanarwar majalisar ya kai ga gudanar da zaman nasa kan wannan batu, rukunin 'yan majalisar dokokin bangaren jam'iyyun adawa na kasar ta Nijar ya fitar da sanarwa ya nisanta kansa daga duk matakin da kwamitin zai dauka, a bisa hujjar cewa ya saba wa doka, domin kuwa ba shi da hurumin yin hakan kamar dai yadda Honorable Abdulkadri Tijjani na jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara ya yi karin bayani.

To sai dai da yake mayar da matani a kan wannan korafi na 'yan majalisar dokokin bangaren 'yan adawar Honorable Ben Omar Muhamed ya ce matakin ba sabon abu ba ne a Nijar.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Pinado Abdu Waba