1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an gaza kyautata ilimi

Mohammad Nasiru Awal/MAApril 9, 2015

Hukumar UNESCO da ke kula da sha'anin Ilimi ta ce kashi biyu cikin uku na kasashen duniya ba su cimma burin da suka sanya gaba na kyautata harkokin ilimi a kasashensu.

https://p.dw.com/p/1F5bO
Kenia Digitales Leben
Hoto: Till Muellenmeister/AFP/Getty Images

A rahoton da ta fitar a wannan Alhamis game da matsayin ilimi a duniya, hukumar ilimi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta ce kashi biyu cikin uku na kasashen duniya baki daya ba sa cimma burin da suka sanya gaba na kyautata ilimi.

A nahiyar Afirka kuwa ana ganin bunkasa ilimin kwamfiyuta zai taimaka wajen magance wannan matsala. To sai dai a kasar Kenya ga misali, ba a samu daidaito ba tsakanin masu kirkirar manhajar kwamfiyuta da shugabannin siyasa kan hanyar da za a bi don kaiwa ga ci.

Tonee Ndungu
Matashi Tonee Ndungu da ya kirkiri manhajar Kwamfiyuta a kasar KenyaHoto: Kytabu

A lokacin da Tonee Ndungu dan kasar Kenya mai shekaru 35 ya ke makaranta ba shi da hazaka sosai, ba ya fahimtar abubuwa masu saukin ganewa ga sauran takwarorinsa 'yan makaranta, inda ya ke cewar "malamai na sun sha fadin min cewa akwai hikima cikin maganganun na kuma na san abin da nake fadi. Amma idan aka zo wajen jarrabawa sai in kasa gane wasu abubuwa masu sauki. An dauki tsawon shekaru kafin a gane cewa ina da matsala wajen karatu. Kwakwalwa ta na iya gane zane fiye da lambobi. Wato ina da kokari wajen zane fiye da lissafi."

Tsarin ilimin Kenya dai bai da amsa ga irin wannan raunin karatu da rubutu. Saboda haka Tonee Ndungu ya fara neman hanyar taimakon kansa da kansa. Ya fara karanta littattafai da karfi ya na kuma daukan sautinsa a kaset. Abu ne mai wahala, amma da wannan dabara ya iya kammala sakandare har ma da jami'a.

Kytabu App
Manhajar da Tonee ya kirkiroHoto: Kytabu

Masana a duniya na kokarin gano yadda za a shigar da sabbin fasahohin zamanin cikin tsarin ba da ilimi. A nahiyar Afirka shirin na Kytabu na daukar hankalin mahalarta taron shekara-shekara kan inganta ilimin ta na'urar Kwamfiyuta. Rebecca Stromeyer mai kamfanin Kwamfiyuta kuma kwararriya a fasahar sadarwar zamani ce ta kirkiro da taron, kuma ta ce manhajar ga wayoyin salula za ta yi kasuwa.

A duniya baki daya an gabatar da shirye-shirye kamar na samar da na'urar Laptop ga ko wane yaro da zumar ceto yara daga matsalar talauci. Sai dai masana irinsu Rebecca Stromeyer, na shakka game da damarmakin da intanet da nau'rorin tafi da gidanka za su iya bayarwa. Kasancewa wayoyin hannun ba su da girma sosai kana kuma ba bu wani bayani dalla-dalla na amfani da su.