1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai yiwuwa akwai sabbin masu Ebola a Mali

Pinado Abdu WabaOctober 31, 2014

Masu bincike kan wadanda suka hadu da yarinyar da ta rasu da Ebola a Mali sun ce akwai masu nuna alamun cutar daga cikin wadanda suka kebe amma ba su gama tantancewa ba.

https://p.dw.com/p/1Df4K
Dousseyni Daou Hospital in Kayes Mali Ebola Kind
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Baba Ahmed

Ana zargin cewa wasu mutane biyu suna dauke da kwayar cutar Ebola a kasar Mali, bayan da suka hadu da yarinyan nan mai shekaru biyu na haihuwa da ta rasu a makon da ya gabata. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya sami wannan labarin ne daga bayyanan da Hukumar Lafiya Ta Duniya ta WHO ta gabatar tare da hadin gwiwan wata cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa na Amirka.

Wasu bayyanan binciken da suka gabatar dangane da wadanda wannan yarinya ta yi ma'amala da su, sun nuna cewa a tafiyar da ta yi daga Guinea zuwa Mali tare da kakarta da 'yaruwarta da kawunta, ta hadu da mutane 141 wadanda a cikinsu har yanzu ba a kai ga gano mutane 57 ba.

Kawo yanzu ana kyautata zaton daya daga cikin 84 da aka kebe yana dauke da kwayar cutar duk da cewa ba a kai ga gwada shi ba, haka nan kuma daga cikin mutane hudun da aka yi wa gwajin, sakamakon ya nuna cewa guda uku ba su da cutar a yayin da ake cigaba da dakon sakamakon mutun guda