1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maharba na taka rawar gani a fannin tsaro

Abdul-Raheem HassanNovember 26, 2014

A Najeriya yanzu haka maharba ne ke taimakawa jami'an tsaro wajen kwato garuruwan da 'yan Boko Haram suka kwace a yankin arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1Dtpl
Hoto: DW/Hassan

Tun kwanakin baya ne maharba da sauran 'yan farauta tare da sa ido na sojoji a yankunan arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya, suka dukufa gadan-gadan wajan yaki da mamayar da 'yan kugiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai ke yi a garuruwa da dama na wannan kasa. Sannu a hankali ta hanyar amfani da saddabaru na gado, maharban ke ci gaba da samun nasara a wannan yaki. Wani daga cikin maharban da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa in an je bakin daga su suna kallon 'yan Boko Haram amma su basa ganinsu. Ya kara da cewa da rokon Allah suke hana bindigar 'yan ta'addan tashi, inda ya ce shugabansu ya daure garin Mubi na jihar Adamawa ne a yayin da suka je ta yadda koda Ashana mutum ya kyasta ba za ta kama ba. Maharban dai kafin su shiga fagen daga domin fafatawa da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram din da ke gwagwarmaya da makamai, sun kware ne wajen farautar namun daji ta yadda suke shiga daji su fafata da dabbobin da suka fi karfinsu.

Maharba sun kwato wasu yankuna na jihar Adamawa daga Boko Haram
Maharba sun kwato wasu yankuna na jihar Adamawa daga Boko HaramHoto: Screenshot royaltimes.net

Goyon baya daga al'umma

Tuni dai al'ummar wannan yanki suka nuna goyon bayansu ga Maharban tare da bukatar gwamnati da ma masu hannu da shuni da su tallafawa Maharaban wajen basu karfin gwiwa a ayyaukan ceto yankunan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace. Sai dai duk kokarin da wakilinmu na Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa da ke Tarayyar Najeriyar Abdul-Raheem Hassan ya yi, na jin ta bakin gwamnati kan yadda suma za su taimakawa Maharban a yakin da suka shiga da 'yan Boko Haram abun ya ci tura. Tuni dai wasu daga cikin shugabannin al'umma suka fara yin kira ga al'ummomin wannan kasa da su tashi tsaye domin su kare kansu daga hare-haren ta'addanci na 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Tarayyar ta Najeriya.