1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya ta zama hanyar bakin haure

Gazali AbdouApril 27, 2015

Dubban bakin haure ke halaka kan tekun bisa yunmkurin shiga Turai

https://p.dw.com/p/1FFWZ
Libyen Auffanglager Zawyia
Hoto: DW/M. Dumas

Bakin haure kimanin dubu da dari shidda ne su ka halaka a cikin teku daga farkon wanann shekara. Duk ta kasar Libiya zuwa nahiyar Turai. Sai dai duk da irin hadarin da ke tattare da wanann tafiya hukumomin Libiya sun kasa iya daukar matakan tsare gabar ruwa.

Libiya ta tamkar wata gada wacce ta raba kasashen Afirka Bakar Fata da nahiyar Turai wacce 'yan Afrika da dama ke bi ta ciki domin zuwa Turai ta hanyar teku.

Libyen Migranten im Abu Salim Zentrum
Hoto: picture-alliance/dpa

Yanzu haka dai jirgin ruwa na aikin ceto daya ne tilo hukumar jami'an da ke kula da tsaron gabar ruwan su ke da shi, wanda haka ya sanya aikin sintirin kan ruwa ya dakata tun a cikin watan Janairu. Kuma sai kawai a lokacin da aka samu labarin wani jirgin bakin haure a teku ne kawai ake iya aiki da shi kamar yadda Mohamed Baithi shugaban hukumar tsaron kan ruwan kasar ya tabbatar.

Libyen Angriff auf süd koreanische Botschaft
Hoto: Turkia/AFP/Getty Images

Bakin haure na da masananiyar hadarin asarar ransu a cikin wannan tafiya inda kusan kowace rana masu kamun kifin ke katarin kamo gawar wani mutum lokacin tattarar komarsu da suka haka dan kama kifi. Sai dai duk da mace-macen da ake samu kowace rana ana samun wasu sabbin bakin haure da ke kasadar kama wannan hanya ta ruwan tekun daga kasar ta Lbiya.