1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya na zaben 'yan majalisar dattawa

Yusuf BalaDecember 20, 2014

Wannan zabe dai an dage shi har sau biyu saboda annobar Ebola da ta addabi kasar da kuma ta yi sanadin kisan sama da mutane dubu uku a kasar ta Laberiya.

https://p.dw.com/p/1E7yR
Wahlen Liberia
Hoto: dapd

Al'ummar kasa Laberiya sun fita kada kuri'arsu a yau Asabar dan zaben cike kujerun majalisar dattawan kasar, a wannan kasa da annobar Ebola ta daidaita.

Wannan zabe da za a cike kujerun 'yan majalisar dattawan 15 an dage shi har sau biyu bayan da annobar Ebola ta mamayi wannan kasa tare da hallaka mutane 3,290.

An dai fara zaben ne da misalin karfe bakwai da rabi a gogon GMT kuma za a kammala shi da misalin karfe biyar na yammaci.

Fitaccen dan wasannan George Weah da ya taka leda a Kulob din Chelsea da AC Milan kafin da ga bisani ya koma gida a shekarar 2003 da dan gidan shugaba Ellen Johnson Sirleaf da wato Robert Sirleaf an daga cikin 'yan takara 139 da suke neman kujeru a majalisar.

George Weah dan shekaru 48 ya gaza samun nasara bayan da ya fito a ka fafata da shi a takarar shugabancin kasar a shekarar 2005 inda suka fafata da shugaba Ellen Johnson Sirleaf.