1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya na ci gaba da yaƙi da cutar Ebola

Yusuf BalaNovember 22, 2014

Laberiya ta ce za ta yi ƙoƙarin tsaida ci gaban kamuwa da cutar Ebola nan da ƙarshen wannan shekara sai dai akwai babban aiki a gaba na tsaida wannan cuta a yammacin na Afirka.

https://p.dw.com/p/1DrXF
Liberia Ebola Info Wand Symptome
Hoto: picture-alliance/dpa/Ahmend Jallanzo

Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim ya yi gargaɗi a jiya Jumma'a cewar, duk da irin nasarar da ake samu a yaƙi da wannan annoba sake samun ɓullar cutar ta Ebola a Mali na zaman babban ƙalubale a ƙoƙarin da ake yi.

Ya ce ya zama dole a gani cewa babu wanda aka sake samu ya kamu da ƙwayoyin wannan cuta, saboda cutar ta Ebola ba cuta ba ce da idan akwai wasu ƙalilan na mutane da suka kamu da ita hankali zai kwanta a ce an shawo kanta .

Shugaba Yong Kim ya bayyana haka ne a yayin taron ƙoli na shugabannin daga Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya da Asusun ba da lamuni na IMF.

Anthony Banbury da ke jagorantar shirin na Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da annobar ta Ebola, ya bayyana wannan annoba da barazana ga ɗaukacin duniya inda ya buƙaci ƙasashen duniya da su ƙara tallafin da ake bayarwa a yaƙi da wannan cuta a Afirka.