1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS na kara samun nasara a Siriya

Salissou BoukariMay 21, 2015

Kwanaki kalilan bayan kame birnin Ramadi da ke a matsayin babban birnin lardin Anbar a kasar Iraki, 'yan jihadi na kugiyar IS sun kama birnin Palmyra a kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/1FTwD
Panzer Syrien IS
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan birni da ke a nisan km 240 a arewacin birnin Damascus, ya shahara ne wajen ajiyar kayayyakin al'adu. A wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Twitter, kungiyar ta tabbatar da kame ga baki dayan wannan birnin, wanda shi ne mafi mahimmanci daga cikin biranen da ta kama a kasar Siriya, bayan wata fafatawa da suka yi da dakarun da ke biyeyya ga Shugaba Bashar Al-Assad.

A cewar kungiyar da ke sa ido kan hakkokin bil Adam ta kasar ta Siriya OSDH mai cibiya a birnin Lodon, 'yan jihadin na kungiyar IS na rike da kaso mafi yawa na kasar ta Siriya. Daga nata bangare kungiyar nan ta 'yan sunna mai biyeyya ga kungiyar ta IS a kasar Libiya, na fadada karfin ikonta a birnin Syrte da ke a matsayin mahaifar tshofon shugaban kasar ta Libiya marigayi Moammar Khadafi.