1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU za ta karfafa hukumomin tsaronta

June 27, 2014

A taron koli da kungiyar AU ta gudanar a Malabo, ta jaddada aniyar Afirka wajen karfafa hukumominta na tsaro da kuma inganta batun noma don wadata nahiyar da abinci.

https://p.dw.com/p/1CRk4
Malabo Gipfel Afrikanische Union Sisi Rede 26.06.2014
Hoto: Reuters

Taron wanda aka shirya da nufin tattauna batun noma da samar da abinci da kuma tsaro, ya fi mayar da hankali a kan barazanar da ake kara fuskanta daga kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da suka addabi nahiyar Afirka.

Da ma dai tun bayan babban taronta a shekarar 2013 kungiyar ta tarayyar Afirka wato AU ta fara tunanin girka wata rundunar gagawa ta Afirka don tinkarar rikice-rikice a nahiyar. Babban buri shi ne samar da dakarun da ke cikin shirin ko ta-kwana da za su fuskanci duk wani rikici ko tashin hankali da zai kunno kai a nahiyar, kamar irin na kasar Mali, da na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wannan runduna ta gagawa mai suna African Standby Force ko ASF a takaice, za ta kasance ta wucin gadi kafin kafuwar babbar rundunar kiyaye zaman lafiya ta Afirka. Matakin dai da kungiyar ta AU ke kokarin dauka, zai bai wa wannan runduna damar gudanar da ayyukanta tare kuma da samun isassun kayan aiki. To ko dakarun Afirka na cikin shirin shiga cikin wannan runduna ta ASF, Farfesa Unnir Abdallah malami fannin shari'a ne a jami'ar Moroco.

"Idan aka fitar da kasar Afirka ta Kudu, da wasu kasashe daya ko biyu na Afirka, dakarun kasashen Afirka ba su da cikakken horo, da kuma kayan aiki, inda a kullu yaumin suke bukatar tallafi daga kasashen waje, na kayan aiki, ko ma na horo da sauran dubarun yaki. A gani na akwai wuya cikin kankanen lokaci a iya kafa irin wannan runduna ta gaggawa a Afirka da za ta iya kula da wanzar da zaman lafiya. Kuma musali idan ma aka dubi ayyukan da sojojin na Afirka ke yi a karkashin inuwar majalisar Dinkin Duniya, sai a ce da sauran rina a kaba."

Magance tarzoma ya zama wajibi

AU Präsidentin Nkosazana Dlamini-Zuma Archiv 16.07.2012
Hoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Shugabar kungiyar kasashen Afirka ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce hare-haren ta'addancin da Najeriya da Somaliya da Kenya ke fuskanta a halin yanzu wata babbar barazana ce ga nahiyar Afirka baki daya.

Ms Dlamini-Zuma ta ce magance hare-haren wani abu da ya kyautu kasashen Afirka su tashi tsaye wajen ganin an yi don gudun kada hakan ya dakushe bunkasar da nahiyar ke yi.

Da ma dai taron na da nufin duba batun noma da wadata nahiyar da abinci, to ko yaya wannan lamarin yake? Christopher Kajoro Chiza shi ne ministan noma na kasar Tanzaniya ya yi karin haske.

"Kamar yadda kuka ka sani kasashen Afirka sun ayyana shekarar 2014 ta zama shekarar aikin gona da samar da abinci. Saboda haka mun tattauna a kan yadda za mu bunkasar harkar noma a Afirka. Har yanzu bunkasar da ake samu a aikin noma na kasa da kashi 4 cikin 100, amma muna son ta kai kashi 6 cikin 100."

Sabbin dubarun noma da tallafi ga manoma

To shin me ya kamata a yi don wadata nahiyar da abinci? Har wayau dai ga minista Chiza.

Gentechnik soll Hunger stillen Bauer bei der Arbeit in Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa

"Dole kasashenmu su fara noma da zai samar da kudaden shiga. Har yanzu nomarmu ta ta'allaka ga kakanan manoma. Dole mu taimaka wa manomanmu da sabbin dubarun noma da tallafin kudi don samar da karin abinci."

Sanarwar bayan taron dai ta jaddada aniyar Afirka wajen karfafa hukumominta na tsaro da kuma inganta batun noma don wadata nahiyar da abinci.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe