1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta dage yanke hukunci a shari'ar Nyako

Mansur Bala BelloSeptember 30, 2014

Mai shari’a Obong Abang ya ce lauya Olanipekun, mai kare gwamnan jihar Adamawa na riko ya kalubalanci shirin hukuncin bayan gano wani kuskuren da aka yi.

https://p.dw.com/p/1DNri
Murtala Nyako
Hoto: DW/U. Shehu

A yau lauyoyi tare da magoya bayan tsigaggen gwamna Murtala Nyako sun shirya tsaf dan jin hukuncin da mai shari'a Obong Abang zai yanke, to amma reshe ya juye da mujiya, inda alkali Abang ya ce lauya Olanipekun, mai kare gwamnan jihar Adamawa na riko ya kalubalanci shirin hukuncin na yau bayan gano wani kuskure da tun farko kafin a sa ranar yanke hukunci ya kamata a saurara.


Yanzu haka dai mai shari'a Obon Abang ya dage yanke hukuncin har sai an saurari bahasin lauyoyin da ke kare gwamna mai rikon kwarya Ahmadu Umaru Fintiri kafin a kai ga yanke hukunci.


A cewar barrister Olukoya Ogunbaje lauya da ke kare tsigaggen gwamna Murtala Nyako, matsayin na babbar kotun ya ba su mamaki, to amma shure- shure ba zai hana mutuwa ba.

Martanin bangaren tsigaggen gwamna Nyako

"Mun zo a shirye dan jin hukuncin da mai shari'a zai yanke, amma mai shari'a ya ce ba zai yanke hukunci ba, ba mu san dalili ba. Za mu ce dage yanke hukuncin da mai shari'a Obong Abang ya yi ba wani abu ne ba illa yankan baya, wanda lauyoyi masu kare gwamna mai rikon kwarya suka shirya mana. Babu ta yadda masu kare kansu za su gabatar da takardar kalubalantar hukuncin inda suke bukatar kotun daukar wani mataki alhali an cimma matsayar yanke hukunci a yau amma lauyoyin gwamna mai rikon kwarya suka kewaya suka sa mu alkali ba tare da an sanar da lauyoyin da suka shigar da kara ba. A sabili da haka za mu yi ma su kamar adda su ka yi mana."

A ranar 11 ga watan Octoba ne za a gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Adamawa, a sa'adda ita babbar kotu za ta yi zamanta a rana 16 ga watan na Octoba. Ma'ana kwanaki biyar bayan zaben gwamna a jihar.

Idan dai ana iya tunawa a cikin watan Yuli ne dai majalisar dokokin jihar Adamawa ta yi zama tare da samun gwamna Murtala Nyako da laifin wadaka da baitulmalin jihar, wani mataki da ya kai ga tsige shi. To sai dai Murtala Nyako ya musanta tare da zargin shirya ma sa tuggu daga sama dan kasancewarsa mai adawa da shugaba mai ci Goodluck Jonathan.

Mutala Nyako tare da mataimakinsa ne kwamitin da majalisar dokoki a jihar ta kafa ta gudanar da bincike a kansu, to amma mataimakinsa Bala Ngilari ya gabatar da takardar yin murabus, gabanin tsige gwauna Murtala Nyako.