1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin tabbatar da mika mulki cikin sauki.

Ubale Musa/ Zainab Mohammed AbubakarApril 23, 2015

Kwamitin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Najeriya na yanzu da wadda ke shirin karbar mulki na tattauna yiwuwar tabbatar da mika mulki ba tare da matsala ba.

https://p.dw.com/p/1FDX2
Nigeria Goodluck Jonathan Abdulsalami Abubakar Muhammadu Buhari
Hoto: DW/Ubale Musa

Wani kwamiti mai wakilai 27 da ya kunshi 'ya'yan APC da na PDP dai ne za su tsara hanyoyin kaiwa ga mika mulkin a watan gobe da ma kudin da kasar ke shirin batarwa a bikin da ma bakin da kasar take shirin gayyata ciki dama waje domin taya ta murnar ranar.

Karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar Anyin Pious Anyim da kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa Timpre Sylva da ke bangaren gwamnatin da ke shirin karbar mulkin dai, 'yan kwamitin za su share makonni har guda shida suna ganawa a tsakanin juna da nufin kai kasar zuwa ga bukata.

Abun kuma da a fadar Senata Bala Abdulkadir Muhammad da ke zaman ministan babban birnin tarraya na Abuja kuma daya a cikin 'yan kwamitin a bangaren na gwamnati, ke zaman alamun gwamnatin da ke barin gadon na dora muradin cigaban kasar a kan gaba.

Ya zuwa yanzu ta bayyana zahiri mulkin kasar ta Najeriya ba zai bar hannun shugaban kasar Goodluck Jonathan ranar 28 ba kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana a farkon fari.

Duk da cewar dai za'a kai ga cin abincin dare a tsakanin shugabannin biyu a ranar 28, ba za'a mika mulkin ba har sai ranar 29 a fadar Patricia Akwashiki da ke zaman ministar yada labaran kasar kuma kakaki ta gwamnati.