1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka na baya a yaki da AIDS

December 1, 2014

Kungiyar ONE ta yi amfani da ranar yaki da cutar Aids ko Sida ta duniya wajen nuna cewar har hanzu da jan aiki a gaban kasashen Afirka na rage yaduwar wannan cuta.

https://p.dw.com/p/1DxQo
Hoto: picture alliance/Yannick Tylle

Hukumar da ke sanya idanu kan yaduwar kwayar cutar HIV AIDS ko kuma SIDA ta Majalisar Dinkin Duniya UNAIDS ta ce an samu ci gaba a wannan shekaraUNAIDS, ta ce an samu ci gaba a bangaren yadda mutanen da ke iya samun maganin rage radadin kwayar cutar ke karuwa. UNAIDS ta bayyana hakan ne a yayin bukukuwan ranar yaki da cutar AIDS ko SIDA da Majalisar Dinkin Duniya ta ware wato daya ga watan Disamba na kowacce shekara.

Rahoton ya nunar da cewa ya zuwa watan Yuni na wanna shekara an samu akalla mutane sama da miliyan 13 da ke samun maganin sabanin miliyan biyar din da suke samun damar a shekara ta 2010.

Sai dai a cewar kungiyar ONE da ke kan gaba na kungiyoyi masu rajin yaki da kwayar cuta mai karya garkuwar jikin a duniya baki daya ta ce hakan bayana nufin an cimma nasara a yaki da cutar bane, domin kuwa wasu kasashen musamman ma na nahiyar Afirka na da sauran tafiya a gabansu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe