1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar masu kaifin kishin addini a Jamus

September 11, 2014

Ana ci gaba da samun kwararar Jamusawa masu zuwa yaki da sunan Jihadi a kasashen Siriya da Iraki. Wannan lamari da na tada hankalin mahukunta dangane da abin da ka je ya komo.

https://p.dw.com/p/1DAVR
Propagandabild IS-Kämpfer
Hoto: picture-alliance/abaca

Wannan lamari ya zama wani abu mai girma cikin shekarun da suka gabata, na samun mayaka da ke kwarara zuwa yaki. Wani kiyasi ya nuna kimanin mutane 12,000 daga kasashen duniya 74 suka shiga cikin yakin da ke gudana a kasar Siriya.

Wani rahoton wata cibiya da ke birnin London na kasar Birtaniya ya ce kashi daya cikin biyar na mayakan Larabawa ne da suka fito daga kasashen yammacin duniya, kuma akwai kimanin 400 daga kasar Jamus.

Salafisten in Deutschland Islam Koran Verteilung
Hoto: dapd

Ga mutanen da suke sane da abin da ke faruwa na matsanancin ra'ayin sun san cewa kasar Siriya yanzu ita ce ta zama 'yan Salafi suna saka a gaba. Mafi yawan kungiyoyin ba sa nuna daukan makami domin shiga tashin hankali da sunan Jihadi, amma tattaunawar ta na biyon baya da Propaganda ta Internet daga kasashen Iraki da Siriya.

Bisa wannan dalilan wasu ke tafiya kasar Siriya, kamar yadda Florian Endres na hukumar kula da baki da 'yan gudun hijira ta Jamus ya nunar. Amma Larabawan da ke tafiya Jihadi daga Jamus ba kasafai suke taka wata mahimmiyar rawa ba a rikice-rikicen da ake samu a kasashen Iraki da Siriya, kamar yadda Marwan Abou-Taam mai bincike kan laifuffukan da ake aikawa masu nasaba da siyasa ya bayyana.

Screenshot Youtube Philipp B. alias abu osama
Hoto: Youtube

Marwan Abou-Taam ya kuma ce saboda basu san al'adun kasashen Larabawa ba, suka zama masu aikata laifi, kuma basu da kwarewa ta aikin soji saboda kalilan daga ciki ne suka taba aikin Soji a Jamus, yayin da mafi yawan mayakan da suka fito daga kasashen Larabawa sun taba aikin soji.

Ba kasafai ake amfani da wadanda suka fito daga Jamus a matsayin 'yan kunar bakin wake ba. Sai dai wata guda da ya wuce Philip Bergner wanda ya Musulunta a garin Dinslaken na nan Jamus ya tayar da bam da ya hallaka shi tare da wasu mutane kimanin 20 kusa da garin Mosul na kasar Iraki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Ahmed Salisu