1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar bullar cutar Ebola a Afirka

August 28, 2014

Hukumomi a nahiyar Afirka na kara matsa kaimi wajen dakile bazuwar cutar nan ta Ebola bayan da aka samu bayanin bullar cutar a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/1D36K
03.09.2014 DW fit und gesund Ebola
Hoto: DPA

Yayin da Tarayyar Najeriya ke cewar ta na dab da cin nasara a yakin da ta daura da cutar nan ta Ebola mai saurin hallaka mutane, sai ga shi cutar ta bulla a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango ko da dai hukumomi a kasar sun ce karfin cutar bai kai wanda ake da ita a yammacin Afirka ba.